Min menu

Pages

Yaki zuwa asibiti za ayiwa matarsa aiki harta mutu

 Wani magidanci yaki zuwa yasa hannu saboda za ayiwa matarsa aiki harta mutuRashin imani ko rashin tausayi ko rashin soyayya?


Ya ki zuwa ya sanya hannu a yi wa matarsa aiki har ta rasu a gadon Asibiti


Wani magidanci ne a jihar Bauchi matar sa ta samu juna biyu na tsawon watanni 9, a ranar Talata ta tashi zata tafi Asibiti wajen haihuwa, sai ya dauko wasu 'yan kudi ya bata, wadanda ko mota baza su ishe ta shiga ba.


Zuwan ta Asibitin sai Likitoci suka fada mata cewa baza ta iya haihuwa da kanta ba doli sai an mata aiki. Daga nan Likitoci suka kira wannan miji nata don su fada masa halin da take ciki, kwana biyu ana kiransa don ya je Asibiti ya sanya hannu a yi wa matarsa aiki amman ya ki zuwa.


Daga karshen dai Allah ya karbi ranta tare da abin da ke cikin ta.


Hakika yakamata wasu maza ku ji tsoron Allah, domin wannan zalunci ne da cin amana.


Sannan ku kuma mata ku dinga sanin irin mazan zaku aura, ku auri maza masu tausayin ku, karku biyewa kudi ko kyan sura.


Ubangiji Allah ya lullube ta rahama

Kunada labarin wani kogi da ake kiransa da kogin mutuwa?

Wani abu yasa magidanci ya kashe matarsa

Comments