Min menu

Pages

Hisbah a kano ta cafke samari da yan matan da basa azumi


Wani magidanci yaki zuwa asibiti za ayiwa matarsa aiki harta mutu

Mutane suna ta hijira zuwa janhuriyar Nijar daga Nijeriya saboda rikicin boko haram

 Hukumar Hisbah a Jihar Kano ta cafke wasu tarin samari da yan mata da basa azumi.


Hukumar tace ta cafke mata a kalla guda takwas da samari uku wanda basa azumin.


Shugaban hukumar yace yanzu haka binciken wadanda aka kama suke domin suji dalilin da kuma hujjar su takin yin azumin.


Tunda dai watan Ramadan ne bai kamata ace karti majiya karfi wanda suke lafiya ba amma suna shan azumi a cewar shugaban yan hisbar.


Ya kara da cewa inda mata ne ta iyu su akwai lokacin da zai kasance baza suyi azumin ba idan suna jinin al'ada.

Comments