Min menu

Pages

Mutane masu yawa sunyi hijira zuwa janhuriyar Nijar

Mutane masu yawa da rikicin boko haram ya shafa sunyi hijira zuwa janhuriyar Nijar. Tarin mutane daga garin damasak wanda rikicin boko haram ya ritsa dasu sun tsallaka kasar nijar kasar da take makotaka da Nijeriya hakan ya biyo bayan yawan kawo musu hare hare da yan boko haram din suke garin nasu.


Majiyar gwamnati tace mutane goma ne suka mutu a harin da yan boko haram din suka kai ranar laraba, inda mutane da yawa sukaji munanan raunuka yayinda da dama daga cikin mutanen suka nausa cikin jeji.


Bayan haka yan boko haram din sun kone gidajen mutane da sauran kayayyaki tare da police station din yan sanda.


Harin da yan boko haram din suka kai jiya garin damasak din dake cikin karamar hukumar mobbar kusan shine na shida a jerin hare haren da yan boko haram din suka kai garin.


Daga karshe dai yan boko haram din sun sake kafa tutarsu a garin kamar yadda wata majiya mai karfi ta rawaito.

Comments