Min menu

Pages

Wani abu yasa magidanci ya kashe matarsa mai juna biyu

 Magidanci ya kashe matarsa mai tsohon cikiWani al'amari ya faru da ya bada mamaki inda wani magidanci yaje har asibitin da aka kwantar da matarsa mai juna biyu ya kasheta.


Al'amarin ya faru ne cikin jihar Lagos inda wani magidanci yaje har cikin asibitin da aka kwantar da matarsa ya kashe ta.


Matar tana dauke da ciki wanda ya girma amma hakan bai hana mijin nata binta har gadon asibitin ba ya kasheta.


Inda majiya ta tabbatar da cewa magidancin zuwa yayi ya cire robar oxygen din da aka sanyawa matar tasa da karfi wanda hakan yai sanadiyar mutuwar tata saboda karancin iskar da zata shaka.


To saidai dama an nuna cewa mijin baya yiwa matar ta sauki domin yana yawan dukanta.


Yan sanda sunyi nasarar kama shi to saidai har yanzu babu takamaiman dalilin da yasa wannan mutumin ya kashe matar tasa.

Comments