Min menu

Pages

Shin kunada labarin wani kogi da ake kiransa da kogin mutuwa

 Shin kunada labarin wani kogi da ake kiransa da kogin mutuwa?



Shine kogi guda wanda duk wani abu mai rai yai kuskuren taba ruwan kogin a take zai daskare ya zama Dutse.


Akwai wani kogi yanzu da yake kasar Tanzania dake Afrika wanda mutane da al'umomi da dama sukai masa lakabi da kogin mutuwa.


Shidai wannan kogin yana da matukar hadari sosai ga duk wani abu da yake da rai domin duk wani wanda ya taba wannan ruwan take yake zama dutse ya daskare, wannan abin yasa ake tunanin kamar akwai wani abu a cikin wannan ruwan.


Hakika abubuwan akwai abin al'ajabi da mamaki kwarai da gaske game da wannan kogin wanda da zarar halitta mai rai ta taba ruwan dake wannan kogin shikenan zata zama kamar dutse ta daskare.


Masu bincike da nazari akan ruwa sunce shi wannan ruwan yanada sinadarin alkalinity da yawa sannan Ph dinsa yakai 10.5 wanda wannan yasa duk wani abu da ruwan ya taba yake saurin daskarewa.


Sunan wannan kogin Natron, wanda yake arewacin kasar Tanzania ruwan gishiri kusan shine asalin sunan da ake ce masa, sannan baya tafiya ko ina saidai tururinsa da hargaginsa ya fita, amma hakan baya hana ruwa ya shiga.

Kogin yanada sinadarai masu yawa wanda suke yin illa ga duk wata halitta zata iya cutuwa idan ta kusanci wajen dan haka muka zo muku da wasu photuna na halittun da suka taba ruwan take suka zama kamar Dutse.


To masu sauraron mu anan zamu dakata ku kasance tare damu a wasu shirye  shiryen na tarihin duniya domin kawo muku labarai da abubuwan mamaki da al'ajabi dake faruwa a Duniya.


Comments