Min menu

Pages

MATAN HAUSA FIM (KANNYWOOD) CIKAKKUN KARUWAI NE – TANIMU AKAWU

 MATAN HAUSA FIM (KANNYWOOD) CIKAKKUN KARUWAI NE – TANIMU AKAWU Ba Zan Iya Auren 'Yar Fim Ba


Shahararren jarumin wasan Hausan nan Tanimu Akawu, yayi wata babbar magana a wata hira da yayi da wani gidan rediyo dake birnin Abuja.

Jerin sunayen mutanen da aka kashe a hanyar Jos

Ya bayyana cewa yanzu babu wani abu da matan ke yi idan ba bin mazan banza masu kudi ba da kuma masu mulki ba.


Jarumin ya bayyana cewa motar da Hadiza Gabon ke hawa kadai za ta iya siyan motocinsa guda goma, ya kara da cewa shi EOD ce yake hawa kuma ya siye ta da kudinshi.


Jarumin ya kara bayar da misali da jaruma Maryam Yahaya, ya ce, “Kallo kawai ta zo yi aka sanyata a cikin fim din Mansoor, amma yanzu wayoyin dake hannunta sun kai na kimanin dubu dari takwas, kasan kuwa ba a fim ta samu wannan kudin ba, saboda nawa ne duka ake biya a fim din?”


Ya cigaba da cewa, “Ko ni yanzu ka bani ‘yar fim na aura bazan aure ta ba, saboda na san abinda ke tafiya a harkar, yarinya tun ba ta da wayo take kallon mu muna yin fim amma yanzu ta zo cikin shekara daya ta samu kudin da bamu taba tunanin zamu samu ba, yaya za ayi ta dinga ganin girman mu.


Mai gabatar da shirin Sabitu Garba Mustapha yayi mishi nuni da cewa wannan magana da yake yi babbar magana ce, inda ya bayyana mishi ya kamata ya tabbatar da abinda yake fada, sai jarumin ya bayyana cewa ai wannan abu kowa ya riga ya sani.

Comments