Min menu

Pages

Shari'ar Abduljabbar Kabara: An ɗage sauraron ƙarar malamin zuwa wannan lokacin

 Shari'ar Abduljabbar Kabara: An ɗage sauraron ƙarar malamin zuwa 2 ga Satumba, 2021Kotun shari'ar Muslunci a jihar Kano ta Alƙali Ibrahim Sarki Yola da ake gidan sarki kofar kudu a yau Laraba ta ɗage sauraron ƙarar Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara zuwa 2 ga Satumban 2021.


Gwamnatin jihar Kano ce ta shigar da ƙarar Malam Abduljabbar kan zarginsa da yin kalaman ɓatanci ga Annabi SAW, Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a faɗin ƙasar tsakanin malamai da musulmai. 


Mai Shari'a Sarki Yola ya ce ya ɗage sauraron ƙarar ne saboda duk hujjojin da aka gabatar sun yi masa tsauri ya yanke hukunci nan take. Sannan yaa ƙara da cewa akwai bukatar ya sake duba su, sannan ya san matsayar da zai ɗauka kan sabbin tuhume-tuhumen da gwamnati ta gabatar a zaman kotun na yau kan Sheikh Abduljabbar, ko kuma duba yiwuwar amfani da iya tuhume-tuhumen farko da aka gabatar.


Lauyoyin gwamnati sun buƙaci a ba su dama su karanto sabbin tuhume-tuhumen da suka je da su a kan Sheikh Abduljabbar, amma lauyoyin Malam Abdujabbar sun soki hakan, sun ƙalubalanci takardar sabbin tuhume-tuhumen da lauyoiyin gwamnati suka gabatar.


Barista Saleh Bakaro wanda shi ne lauyan da yake jagorantar ɓangaren Abduljabbar bayan yayi sukar, ya ƙara da cewa gaba daya lauyoyin SAN din da gwamnati ta dauko ba su da hurumi a tsarin dokar aikin lauya na shiga ƙaramar kotu.


"Daga babbar Kotun Tarayya ne aka yarda SAN su fara zuwa kotu. Sannan sabbin tuhume-tuhumen da suka bayar ya saɓa da tsarin dokar shari'ar Musulunci" inji Bakaro


Ya cigaba da cewa "Ba a yarda mutum ya sake shigar da tuhuma ko ƙara kan wata da ake saurara ba, bayan gabatar da shaidar farko a tsarin dokar Shari'ar Musulunci," 


Su kuwa lauyoyin ɓangaren gwamnati sun ce kamata ya yi lauyoyin Abduljabbar su dakata a gama karanto sabbin tuhume-tuhumen da ake yi wa wanda ake ƙarar kafin su kawo wata suka kan lamarin.


Sun ce a bisa doka wajibi ne a karanto cajin wanda idan an kammala ne sannan wani bangare zai iya suka ko goyon bayan a ci gaba da shari'a.


Barista Surajo Sa'ida SAN mai jagorantar lauyoyin gwamnati ya dogara ne da Sashe na 390 ƙaramin sashe na biyu na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda a don haka ya buƙaci lauyan Abduljabbar ya janye sukar da ya yi har sai bayan an kammala karanto sabbin tuhume-tuhumen da suka gabatar wa kotu.


Lauyoyin Abduljabbar sun ce sashen da lauyoyin gwamnati suka dogara da shi, na magana ne kan cajin da aka gabatar tun ranar farkon ranar da aka gurfanar da Abduljabbar a kotun ranar 16 ga watan Yunin da ya gabata.


A ranar fara sauraron ƙarar an karanta masa tuhumar da ake masa ne ta farko ta 'yan sanda, wanda kuma bai amsa aikata laifin ba, don haka ya riga ya amsa ƙara, wanda hakan ke nuni da an fara shari'a.


A ƙarshe dai mai Shari'a ya ɗage ƙarar zuwa 2 ga watan Satumba, 2021 dan cigaba da Shari'a.

Comments