Min menu

Pages

Budurwa ta gayyaci kawayenta wurin cin abinci da saurayinta, sun ci abinci saurayin ya gudu

 Budurwa ta gayyaci kawayenta wurin cin abinci da saurayinta, sun ci abinci saurayin ya guduNa dauki aniyar gogawa maza 2000 cutar kanjamau – Budurwa


WATA SABUWA~ Mansurah Isah Ta Yi Allah-ya-isa Kan Mutuwar Auren Ta


– Wata budurwa ‘yar Najeriya ta yi wata wallafa ta bayyana abinda ya faru da ta je wurin cin abinci da kawayenta da saurayi

Ta bayyana yadda ta kwashi mugun takaici a Twitter sakamakon abinda saurayin yayi mata

Sai da ya cinye abincin shi tas, ya biya kudinsa sannan ya kara wa motarsa mai ya kyalesu a wurin

Budurwa ‘yar Najeriya ta kwashi kawaye zuwa wurin cin abinci tare da saurayinta da niyyar ya biya musu kudin.


A cewarta, ta fita tare da saurayinta da kawayenta biyu, amma ya gewaye ya biya kudin abincinsa ya kara wa motarsa mai.


Kamar yadda tayi wallafar a ranar Juma’a, 8 ga watan Janairu inda tace lallai akwai mugayen maza a duniya. Ta ce halin saurayin ya nuna rashin sanin ya kamata.


A cewarta, akwai mazan da suke girmama kawayen ‘yan matansu saboda soyayya. Take anan aka fara cece-kuce a karkashin wallafar.


Wani laoluakanni yace: “Wannan ne dalilin dake sanya wa mata su rabu da wanda ya kamata su so da zuciya daya saboda kawaye. Idan fa gayen ya fara son daya daga cikin kawayenki? Shikenan kin rasashi. Gara ki tafi daga ke sai shi, ba tare da wata kawa ba. Ya kamata mata ku yi wayau a shekarar 2021.”


Wani Isreal45697763 yayi tsokaci da: “Idan ya san ya kamata, kema ya kamata kisan yadda ya kamata. Idan ya bukaci ku fita, kada ki debo gayyar kawaye.”


GailAllan15 cewa tayi: “Ya yi min daidai. Ya kamata ki tambaye shi don ya san nawa zai zo da shi, idan zai iya biya wa kawayenki sai yazo.”


Comments