Min menu

Pages

Na dauki aniyar gogawa maza 2000 cutar kanjamau – Budurwa

 Na dauki aniyar gogawa maza 2000 cutar kanjamau – Budurwa


Jerin jahoji da sukafi yawan masu cutar kanjamau (HIV) a kasar Nigeria

Wata kyakkyawar budurwa ‘yar jami’a ta dauki alkawarin gogawa sama da mutum 2000 cutar kanjamau

Budurwar ta dauki wannan aniya ne a matsayin neman fansa da take yi na goga mata cutar da wani ssaurayi ya yi ba tare da saninta ba

Ta ce babu wani abu a duniya da zai hana ta cika wannan buri na ta da ta sanya a gaba

Wata matashiyar daliba da take karatu a jami’ar Kabarak dake Nakuru, a kasar Kenya ta bayyana yadda ta gogawa sama da maza 324 cuta mai kashe garkuwar jiki wato Kanjamau, haka kawai da gangan da ganganci.


Matashiyar dalibar ta bayyana cewa ta dauki niyyar gogawa sama da maza 2000 wannan cuta, saboda ta dauki fansa akan wani saurayi da take tunanin shine ya goga mata cutar a wajen casu.


A wani rubutu da ta yi a shafin sadarwa na zamani, ta bayyana cewa ba za ta taba mantawa da ranar 22 ga watan Satumbar shekarar 2013 ba, a lokacin da aka goga mata wannan cuta ta kanjamau.


Budurwa ta yi alkawarin gogawa maza 2000 cutar Kanjamau

Sun yi amfani da damar su sun goga mata cutar kanjamau yayin da ta sha giya ta bugu

Ta bayyana cewa a lokacin da ta tashi daga bacci da safe ta shiga za tayi wanka ta gane cewa anyi amfani da ita ba tare da amfani da abin kariya ba wato karoron roba, a lokacin da take cikin mayen giya.


Daga baya ta gano cewa tana dauke da cutar ta kanjamau, inda ta tunkari wani saurayi mai suna Javan, wanda ya bayyana mata cewa shi babu ruwan shi a wannan hali da ta shiga.


Kawai na tambayeshi ne ko yayi amfani da kwaroron roba, sai dai kuma a lokacin da nake wanka, na ga alamun maniyyi a jikina. Na yi kokarin kashe kai na, naji tsoron yin ciki ko kuma kamuwa da cutar HIV.


A lokacin dana gano cewa ina dauke da cutar, na shiga cikin damuwa, nayi ta shan giya domin na mutu, har guba na siyo domin na sha na mutu, na rasa yadda zan kalli iyayena, na riga na san an riga an bata mini rayuwa har abada, sai dai na saka a raina cewa sai na rama.


cewar budurwar

Ta kasa komawa ta kalli iyayenta a wannan hali da take ciki, haka kuma ta rasa yadda za ta kalli sauran mutanen duniya da wannan cuta.


Ramuwa

A lokacin da ta bayyana wannan hali da ta shiga ta riga ta gogawa sama da maza 324 cutar, inda kimanin rabi daga cikin su duka daliban wannan makaranta da take ne. Haka kuma a cikin mutanen da ta dau aniyar gogawa akwai ‘yan siyasa, taurari, malaman jami’a, lauyoyi, da kuma mazaje masu aure.


Na riga na dauki kaddara, sai dai nayi alkawarin duk na mijin da ya rabe ni sai ya gogi cutar, na san cewa ina da kyau da daukar hankali, maza da yawa na kokarin ganin sun jawo hankalina.


Ta kara da cewa babu ranar da take zuwa ta wuce ba ta kwanta da namiji ba, wasu ranekun ma har maza 4 take kwanciya da su, inda hakan ya zame mata tamkar al’ada 


Ta kara da cewa babu abinda zai hana ta cimma wannan buri da ta sanya a gaba. A karshe ta bayyana cewa:


Maza sun bata mini rayuwa, saboda haka sai na tabbatar ku da iyalanku kun girbi abinda kuka yi mini.

Comments