Min menu

Pages

BUDURWA TA GUJI SAURAYINTA BAYAN YA RASA AIKINSA

 

Saurayi da budurwar shi ta guje shi bayan an kore shi a aiki, ya mallaki kamfanin kanshi
Wani matashin saurayi dan Najeriya ya burge masu amfani da shafukan sadarwa akan yadda lokaci daya Allah ya albarkaci rayuwar shi, bayan ya fuskanci matsaloli irin na rayuwa.

Saurayin mai suna Victor Anangwe ya hau shafin sadarwa  ya wallafa yadda yayi kokarin hakura da komai na rayuwa a shekarar 2017 sakamakon rasa aikin shi da yayi.

Victor ya ce a wancan lokacin budurwar shi ta guje shi, inda ya rame sosai sakamakon hakan. Da yake wallafa hoton shi a shekarar 2017, saurayin ya ce ya rame daga 72kg zuwa 53kg.

Sabuwar rayuwa ga Victor

Allah ya daukaka shi a lokacin da ya fara tallar gidaje da na’ura mai kwakwalwa ta abokin aikin shi, inda a lokacin mahaifiyar shi ce ta taimaka masa da kudin da ya sayi data yake hawa.

A yau Victor, Allah ya taimake shi, abubuwa suna tafiya dai-dai a kamfaninsa mai suna Kareps.

Comments