Min menu

Pages

WATA SABUWA~ Mansurah Isah Ta Yi Allah-ya-isa Kan Mutuwar Auren Ta

 WATA SABUWA~ Mansurah Isah Ta Yi Allah-ya-isa Kan Mutuwar Auren Ta 


Na dauki aniyar gogawa maza 2000 cutar kanjamau – Budurwa



“Allah ka saka min. Allah abin da su ke min ka yi musu, ka yi wa yaran su, iyayen su, ‘yan’uwan su. Allah ka jarabce su da ƙuncin rayuwa na aure domin su gane kuskuren su. Amin ya Allah.”


TARE da waɗannan zafafan kalamai, fitacciyar jaruma mai ritaya, Mansurah Isah, a daren yau ta yi Allah-ya-isa ga mutanen da su ke aibanta ta a soshiyal midiya saboda mutuwar auren ta.


Idan kun tuna, a ranar 28 ga Mayu, 2021 mujallar Fim ta ba ku labarin mutuwar auren Mansurah da fitaccen jarumi kuma mawaƙi Sani Musa Danja.


Akwai ‘ya’ya huɗu a tsakanin su – mace ɗaya, maza uku.


Mutuwar auren ta girgiza mutane tare da jawo ka-ce-na-ce a soshiyal midiya, inda mutane su ka dinga tofa albarkacin bakin su.


To ban da masu taya Mansurah alhini, akwai masu zagin ta, ashe ma wasu har ta hanyar saƙon kai-tsaye gare ta ta bayan fage, wato ‘direct message’ ko DM.


A kan masu irin wannan aibanta ta ɗin ne Mansurah ta tura saƙo na musamman a Instagram a yau, inda ta jawo hankalin su ga munin abin da su ke aikata mata.


A cewar ta, ɓatancin da su ke yi mata ya na taɓa rayuwar ta ta hanyar da ba su zato.


A saƙon mai shigen fosta, wanda ta yi da salon ingausar Hausa da Turanci, wanda kuma mujallar Fim ta fassara, Mansurah ta fara da cewa ta lura da yadda duk motsin da ta yi a soshiyal midiya tun bayan mutuwar auren ta sai wasu ‘yan sa ido sun soke ta a kai. “Yara, har da tsofaffi fa, har DM su na zagi na,” inji ta.


Kafin ta wallafa saƙon ta na Allah-ya-isa, sai da Mansurah Isah ta bada sanarwar ta na rubuta wani saƙo da za ta tura

Ta ce: “Na yi hoton Sallah, kun ce abin da ya sa na fito kenan. Na yi tafiya zuwa wani gari, kun ce shi ya sa na kashe aure na. Na je cin abinci da ƙawaye na, kun ce iskancin da na ke son yi kenan. Na je aikin NGO na rabo da na saba yi yau wajen shekara 20 kenan ina yi, kun ce da man yawon da ya fito da ni kenan.”


Ta ce akwai masoyan ta waɗanda za su so ta yi haƙuri kada ta tanka wa irin waɗannan mutanen, to amma fa rayuwar ta ce ake taɓawa kuma ta na da ‘yancin ta yi abin da ta ga damar yi da rayuwar ta. 


Ta tambaye su da cewa shin kalmar “saki” ce “ba ku taɓa ji ba ne, ko kuma ba ku taɓa ganin mace da aka saka ba?”


Da ta dubi batun mutuwar auren nata ta fuskar addini kuma, sai ta faɗa wa masu kushe ta cewa, “Annabin tsira (SAW) ya taɓa sakin mace. Allah da ya halicce mu ya halasta (saki). 


“Me ku ke so a matsayin mu na muminai da bin dokokin Allah? Umarnin ku za a bi ko na Allah?”


Ta ƙara da cewa, “Ni dai na san ban yi wa kowa laifi ba. Wasu har da buɗe sabon ‘account’ don su zage ni. Haka nan kawai.”


Tsohuwar jarumar kuma shugabar ƙungiyar agaji ta ‘Today’s Life Foundation’ ta ce in dai batun saki ne, ai ba kan ta farau ba. “Ba ni kaɗai ba ce mace mai aure ko wacce aka saka a soshiyal midiya’ ba.”


Bugu da ƙari, ta yi nuni da yadda mutane ‘yan sa ido ba su cewa uffan kan ‘ya’ya mata da ake gani cikin shigar rashin mutunci a soshiyal midiya, sai ‘yan fim kaɗai ake wa kwakwazo. Ta ce da su, “In kun ga yaran masu kuɗi tsirara ba ɗankwali a kan su, ko su na abin da su ka ga dama a soshiyal midiya, ku yabe su, in ‘yar fim ta yi daidai irin wannan ɗin ku zage su. Kun yi wa kan ku adalci kenan? Ku ji tsoron Allah wallahi.”


Mansurah ta yi kira ga masu sukar ta ɗin da su dubi kan su tukuna kafin su yanke mata hukunci. Ta ce, “In kun koma gida ku tambayi ‘yan’uwan ku mata, ko uwayen ku ko maƙwabtan ku da aka taɓa saka, su faɗa maku yadda su ke ji, ku tambaye su faman da su ke yi da rayuwa. Su ba ku amsa, sannan ne za ku san abin da ku ka yi mani.” 


Haka kuma Mansurah Isah ta yi rantsuwar ba za ta yafe wa duk wani wanda ya zage ta ko ya aibanta ta ba.


Cikin kausasan kalamai, ta ce: “Ba zan taɓa yafe wa duk wani wanda ya musguna wa rayuwa ta ba. Allah ya isa. Allah ka saka min.”


A ƙarshe, Mansurah ta roƙi Allah da ya bi mata haƙƙin ta a kan su. Ta ce: “Allah abin da su ke min ka yi musu, ka yi wa yaran su, iyayen su, ‘yan’uwan su. Allah ka jarabce su da ƙuncin rayuwa na aure domin su gane kuskuren su. Amin ya Allah. Amin don wata mai albarka da mu ke ciki. Amin ya Allah.”


Wannan dai shi ne karo na farko da Mansurah ta fito ɓaro-ɓaro ta yi magana kan mutuwar auren ta tun bayan sanarwar farko da ta wallafa inda ta bada sanarwar tsinkewar igiyar auren.



Comments