Min menu

Pages

Jerin kasashen Afrika da ake iya zuwa da mota

 Jerin kasashen Afrika da ake iya zuwa da mota
Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da wannan lokacin ya kuke ya aiki? Muna fatan komai yana tafiya daidai.

A yau cikin shirin namu na zagaya duniya muna tafiya muku ne da batutuwa akan wasu tambayoyin da ake ta famar yi mana cewa wadanne kasashen ne ake iya zuwansu a mota ba sai mutum ya hau jirgi ba.

Kasancewar kudin jirgi yanada yawa hakan yasa mukai bincike muka zakulo muku sunan wasu kasashe da zaku iya zuwa a mota bawai sai a jirgin kasa ba.


Nasan da yawa sunada bukatar barin kasarsu zuwa kasashen dake makota damu domin su gaisa da abokansu ko kuma suga yan matansu wasu kuma harkar kasuwanci yasa suke son fita zuwa wata kasar saidai basu iya zuwa ba saboda basu da kudin jirgi ko kuma yayi yawa.


To yanzu dai cikin hukuncin ubangiji ga jerin sunayen kasashen nan da zaku iya hawa mota kuje ba tare da tsada ko bata lokaci ba.


Jerin kasashen da zaku iya zuwa a mota a nahiyar afrika ba sai kun hau jirgi ba.

√ Ghana 


√ Togo


√  Mali


√ Benin republic


√ Nijar√ Mouritania

√ Chad


Wadannan kasashen kowanne dan Nijeriya zai iya zuwa a mota duk da cewa wasu guraren suna da dan nisa amma dai suna zuwa a mota sannan akwai wasu kuma sai an dan shiga ruwa

Comments