Min menu

Pages

Wata mata ta turawa mijinta albashinta gaba daya sannan ta fada masa wata magana akan yadda zaiyi da kudin

 Wata mata ta turawa mijinta duka albashin data dauka.Kafafen yada labarai sun rikice tun bayan da aka samu labarin wata mata da ta turawa mijinta duka kudin albashin data dauka.

Wata mata ta zazzagi Buhari a London

Matar da take amfani da suna @ jagzangel a twitter ta rikita mutane saboda abinda ta aikata na turawa mijinta duk albashin ta.


Wannan yasa mutane da yawa keta famar fadin albarkacin bakinsu inda maza da dama suka jinjina mata suna nuna irin wannan matar ita ce ake nema yayinda mata kuma wasu ke kushe abinda tayi har suna cewa maza ba yan goyo bane.


To saidai ita a cewarta taimakawa masoyinta ba wani abu bane domin ko shi yana zuwa kasuwa yayi mata sayayya ba tare da ta sani ba ya kawo mata.


Yana mata duk wasu dawainiyar data dace ya ciyar da ita ya shayar da ita.


Lokacinda albashina ya shigo account dina jiya saina kira mijin nawa na fada masa cewar kudina ya shigo dan haka nawa yake so na bashi, ya dauka wasa nake masa sai ya fadi wasu yan kudade kalilan domin yasan babu komai a account dina a da a cewar matar.


Dana tashi sai na tura masa duka kudin na albashin nawa.


Abin ya bawa wasu mamaki ni kuma a guri na ba komai bane domin yana yimin komai da kudinsa kuma zan dage sosai na samu kudi domin na taimaki mijina.

Danna nan domin dauko sabon bidiyon makiri

Danna nan


Mata shin kuna ganin zaku iya wannan kuwa?


Wata jarumar kannywood tace zata kashe kanta ta huta

Comments