Min menu

Pages

Kashe kaina zanyi na huta da wannan rayuwar inji jarumar kannywood Ummi Zee Zee

Kashe kaina zanyi na huta da wannan rayuwar inji jarumar kannywood Ummi Zee Zee Jaruma kuma tauraruwa a masana'antar shirya fina finan hausa wato ummi zee zee tace kuncin rayuwar tayi mata yawa da har take jin tamkar ta kashe kanta ta huta.


Jarumar ta sheke ayarta a lokacinda tauraruwarta take haskawa a masana'antar kannywood domin tayi abubuwa masu yawa domin ta samu kudi kuma tai suna.


Tayi soyayya da manyan mutane masu kudi da kuma manyan samari mawaka harna kudancin kasar nan sannan ta zama yarinyar wasu daga cikin masu kazamar dukiya.


Jarumar tayi suna sosai wanda nake ganin da wuya a samu wacce zata danne sunanta daga cikin jaruman mata na kannywood.


To saidai yau an hangeta tana cewa ji take tamkar ta kashe kanta saboda kuncin rayuwar da take ciki.


Wannan kadai ya isa babban darasi ga yan matan da suka biyewa kudi sama da mutuncinsu.

Comments