Min menu

Pages

SAURAYI YANKEWA BUDURWARSA HANNU SABODA TAKI YARDA YAYI MATA FYADE


 Dalilib da yasa Ya Mutumin ya  Sare Min Hannu Saboda Naƙi Yarda Yayi Min Fyaɗe, Yarinya Ta Bayyana Wa Kotu

Arna sunfi tausayi inji wata yar wasan hausa ummi zee zee

Wata yarinya ƴar shekaru 16 da haihuwa, babbar daliba a Gundumar Bududa, Uganda, ta ba da labarin yadda wani mutum ya tare mata hanya inda ya yanke mata hannu bayan ta bijire wa yunƙurin yi mata fyade.


Evelyn Namasopo ta faɗa wa Babban Magistrate na Mbale, Mista James Mawanda, yayin wani zama a Kotun Majistare ta Bubulo da ke Gundumar Manafwa a ranar Laraba, 7 ga Afrilu, cewa wanda ake zargin Derrick Kuloba, mai shekara 25, ya kai mata hari a kusa da wani daji a kan hanyarta ta zuwa gida don karɓowa mahaifiyarta dake kwance a asibiti abinci.


Evelyn ta ce ta yi kuwa da ihu da fatan samun taimako amma a banza, ta kara da cewa har yanzu tana fama da raɗaɗi mai yawa.


Wacce abun ya shafa tayi zargin ƴan sanda da Kotun Mbale da ƙoƙarin murƙushe ƙararta saboda an saki Kuloba a wani yanayi da ba a san shi ba ƴan kwanaki kaɗan bayan kama shi.


Mai gabatar da ƙara ya shaidawa kotu cewa Kuloba, mazaunin ƙauyen Nabooti, ​​Nakatsi Sub-County a cikin Gundumar Bududa, a ranar 4 ga Yulin, 2020 ɗauke da adduna, ya tare mata hanya kuma ya far mata da niyyar yi mata fyaɗe, bayan taki amincewa sai ya sare mata hannu.


Yarinyar kuma ta samu raunuka da dama a wasu sassan jiki. Mai gabatar da ƙara ya gabatar da shaidu uku; wanda abun ya shafa, ɗan uwanta da kawunta.


A cikin shaidar ta, yarinyar ta ƙara roƙon kotu da ta yiwa Kuloba hukunci mai tsauri.

Wani saurayi ya cinnawa dakin masoyiyarsa wuta

An ɗaga ƙarar zuwa 8 ga Afrilu, 2021 lokacin da ake sa ran mai gabatar da ƙara zai gabatar da ƙarin shaidu a kotu.

Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments