Min menu

Pages

Wallahi Arnan Najeriya Sun Fi Musulman Tausayi, Inji Ummi Zeezee


 Wallahi Arnan Najeriya Sun Fi Musulman Tausayi, Inji Ummi Zeezee


Fitacciyar jaruma Ummi Ibrahim (Zee-Zee) ta bayyana cewa ƴan Najeriya waɗanda ba musulmi ba sun fi takwarorin su musulmi jinƙai.


Ta ce ta gane haka ne daga abin da ya faru a gare ta a makon jiya lokacin da ta yi barazanar za ta kashe kan ta saboda damfarar da aka yi mata ta kuɗi naira miliyan 450.


Zee-Zee ta ce lokacin da abin ya faru, yawancin Hausawa ko ƴan Arewa musulmi daga masu ƙaryata ta sai masu zagin ta, amma su kuwa ƴan Kudu waɗanda ba musulmi ba, waɗanda ta kira “arna”, su ne masu tausaya mata da jajanta mata.


“Sai yanzu na fahimci arnan Najeriya wallahi sun fi Musulman Najeriya tausayi. Don haka Allah wadaran Musulmai masu irin wannan mummunar zuciyar”. Inji Zeezee kamar yadda ta bayyana a shafinta na Instagram


Daga nan ta yi tir da waɗanda su ka zage ta ko su ka ƙaryata ta a kan wannan lamari.

Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments