Min menu

Pages

Yan kudu zasu fadi matakin da zasu dauka akan abinci da naman da ake kai musu daga arewa ranar juma'a

 Yan kudu za suyi zanga zangar daina amfani da naman saniya ranar juma'a sannan sun fadi abubuwan da za suyi kamar haka:-
Zamu daina shigo da goro arewa

Yan kudu zasu gabatar da wata zanga zangar daina amfani da naman saniya da kuma rago ranar juma'a mai zuwa.


Sun fitar da wannan sanarwar ne ta bakin wasu yan kudun kamar irinsu Sunday Igboho da sauran mutanen yankin nasu.


Wannan ya biyo bayan shiga yajin aikin da masu kaiwa abinci yankin kudun suka shiga saboda wasu fitunu da yan kudun suka tasa wanda har takai an kona wasu kayayyaki na yan arewa.


In baku manta ba tun wajen kwana hudu da suka wuce manoma da sauran yan kasuwa masu shigar da abinci da nama kudu suka shiga wani zazzafan yajin aiki na daina kai kaya kudu wanda hakan ya jawo maganganu da dama wanda yan arewa suke ganin kamar badan dasu ba da tuni babu yan kudun domin abincin ma daga arewa ake kaiwa yan kudun, to saidai yan kudun suna ta fadar maganganu ga yan arewan inda har cewa suke suma ai sunada abubuwa da suke shigo dasu arewa kamar goro da kwakwar manja dan haka zasu rike kayansu.


Bayan haka kuma sun sanar da ranar juma'a amatsayin ranar da zasu daina amfani da naman saniya ko sa da sauran naman da ake shigar musu dasu yankin nasu.


To saidai yan arewa suna ganin koda yan kudun sun daina shigo musu da wadannan kayayyakin su baza su takura kamar yan kudun ba.

Comments