Min menu

Pages

Zamu hana shigo da goro arewa inji yan kudu

 Muma zamu hana shigo da goro da kwakwar manja arewa.Yan kasuwar kudu sun kufula harma suna cewa zasu hana shigo da goro arewa tunda suma an hana shigar da abinci da nama kudu.


In baku manta ba a yan kwanakin nan aka dakatar da shiga da abinci da dabbobi kudu biyo bayan wani sabani da aka samu wanda wasu daga cikin yan kudun suka kone motocin abinci da dama na yan arewa.


Wannan abin bai yiwa yan kudu dadi ba domin yanzu haka abinci ya fara wuya matuka a kudu.


Yadda kayan miya ko nama baya iya sayuwa a gun wasu.


To sai yau muke samun labarin cewa suma sunce zasu hana shigo da goro dama kwakwar manja arewa domin su rama abinda yan arewa sukai musu.


Saidai wannan hukuncin da suka yanke ya bewa yan arewa da dama dariya domin sunce su da suke da dabino me za suyi da goro.


Comments