Min menu

Pages

Wani Mutum ya yanke azzakarinsa saboda ya gujewa aikata zina

 YAWAN SON YIN JIMA'I YA SAKA WANI MUTUM YANKE AZZAKARISA DOMIN GUJEWA YIN ZINAAn sami labarin Wani mutum a jahar Benue daya kashe azzakarinsa domin ya tsare Kansa daga yawan son aikata jima'i.

Mutumin mai suna Terheman Anonga, Wanda akafi kira da suna Doc k ko kuma Bob korna, yace abune mai kyau ka rabu da duk wani abu dazai rika jawo maka aikata zunubi daga karshe ka kare a wuta bayan ka mutu, Kamar yadda littafin Bible ya bada umarni.

Mutumin mazaunin Gboko, cibiyar tiv, Anonga yace yana da matukar wahala mutum ya iya jurewa aikata zina a wajen da ake samun tsiraici a ko yaushe.

Anonga ya samu wasu mutane masu tsananin ruko da addini dasuka biya masa kudi likitoci suka cire masa 'yayan marainansa domin ya maida hankali sosai wajen yin bauta.

Anonga an koreshi daga jami'ar likitanci ta Ibadan a 2007 shekarar sa ta karshe bisa dalilai na tabuwar kwalkwaluwa. Yana zaune shi kadaine a gidan mahaifinsa, ya kori duk wasu makusantansa bisa zarginsu da yimasa shishshigi.

Mazauna Gboko na ganin Anonga a matsayin mutum mai iya furuci,ilimi tare da matukar biyayya.

Saboda rashin aiki da Anonga ke fama dashi yakan dauki kayan trader a wheelbarrow ya sayar ya samu abin biyan bukatu. Anonga a koda yaushe yana cikin karanta Bible da kuma jaridu wadanda suka danganci addini.

Comments