Min menu

Pages

Nura m Inuwa ya sanar da sunan sabbin albums dinsa na wannan shekarar

 Nura m Inuwa ya sanar da sunan sabbin albums dinsa na wannan shekarar

Manyan labarai


Shahararren mawakin nan Nura m Inuwa ya sanar da sunan sabbin albums din wakokinsa guda biyu da zai fitar a wannan shekarar kamar yadda ya wallafa a shafinsa na facebook.


Mawakin dai shine wanda a kwana kwanan nan masoyansa suka fara fitowa cikin kafafen yada labarai suna yin zanga zanga akan rashin sakar musu da wakokinsa da yace zaiyi cikin wannan shekarar, inda har wasu ke ta cewa sun gaji da jira.

Watakila wannan ne yai saurin jawo da hankalin mawakin har ya fito musu da sunan albums din na wakokinsa guda biyu.

√ Lokaci

√ Ni da ku

Wadannan sune sunan albums din nasa wanda yace zai fito da fostocinsa nan da dan wani lokaci kankani, sannan ya sake bewa masoyansa hakuri na cewa yana kan gabatar da aikin kuma insha Allahu bazai basu kunya ba.


Comments