Min menu

Pages

Shin kunsan wadannan mahimman wuraren a Nigeria?

 Muhimman wuraren shakatawa da bude ido a Nigeria

Kamar kowacce kasa Nigeria ma ta biyo sauran kasashen wajen samun kayattun guraren shakatawa wanda mutane daban daban na cikin kasa dama sauran kasashen ketare kan ziyarta domin bude ido da debe kewa.

Idan kuna biye damu zamu nuna muku Duk kan guraren daya bayan daya tare da bayaninsa.

Guraren shakatawar gasu kamar haka:-

1. Jigayin Mambilla 


Jigayin mambilla a jihar Taraba suke dake a arewacin Najeriya, jigayin mambilla suna da yanayi mai ban sha'awa tare da jan hankali mutum matuka, jigayin sun fara daga mambilla ta jihar Taraba har zuwa tundun Bamemda dake cikin kasar kamaru. Tudun mambilla yana da akalla tsawon meter 1,600 daga kasa Wanda hakan ne yasa yafi kowane hawa(Tudu,jigawa,) tsawo a Najeriya.

2.Magangarar marafa.


Magangarar ruwan marafa a jihar plateau yake a karamar hukumar Bassa ,wannan waje,gurine da ruwa ke gangarowa daga saman duwatsu yana gudana zuwa cikin koramu.

3. Tsibirin Obudu


Obudu tsibiri ne dake a jihar cross river,obudu waje ne mai matukar girman kasa da kuma fadi, obudu yana daga cikin wuraren shakatawa a Najeriya da za'a iya kira makura. Tafiyar awa shida ce daga cikin calaba, babban birnin jihar cross river zuwa wajen.

4. Dajin Sumu

Dajin sumu daji ne a karamar hukumar Ganjuwa, Jihar Bauchi,Dajin nada murabba'in kilomita 82, an bude wajen a 2006 a karkashin tsarin hadin gwiwa tsakanin Kasar Najeriya da Kasar Nimibiya.

5. Dajin Gashaka Gumti, jihar Taraba. 


Dajin Gashaka babban dajin halittu ne a Najeriya Wanda keda girma murabba'in kilomita 6,402, dajin yana kan iyakar Najeriya da kamaru da kuma wasu manyan wurare irinsu chappal waddi Wanda yake da matsayin mita 2,500.

6. Ruwan wikki, jihar Bauchi.

Ruwan wikki ruwane a cikin babban dajin nan na Africa dake a Najeriya wato dajin yankari. Ruwan wikki a koyaushe yanayin duminsa baya canjawa daga 32 na ma'aunin yanayin dumi Wanda hakan ya Sanya ruwan yake da dadin wanka a koda yaushe.

7.Dausayin yusufari, Jihar Yobe.

Dausayin yusufari wata rayayyiyar sahara ce mai ni'ima a jihar yobe karamar hukumar yusufari, ance wannan wajen shine kadai akafi  samun sinadarin Gem(Wanda akeyin kayan alatu na kwalliyar mata kamar yan kunne da sauransu), tarihi ya kuma nuna cewa asalinwajen, waje ne da masu saida kanwa ke yada zango da rakumansu

8.Husumiyar Kujuru,Jihar Kaduna.


Wannan husumiya irin ta dace wanda wata kungiyar yan kasar Jamus suka gina, an gama Gina wannan husumiya a shekarar 1989 bayan anyi shekara takwas ana faman gininta. Tafiyar minti  45 ce daga Kaduna zuwa wajen, wajen an maidashi wajen shakatawa ga masu yawan bude ido.

Comments