Min menu

Pages

Jerin masu kudi guda bakwai da aka binne su da dukiyoyinsu

 Jerin masu kudi guda bakwai da aka binne su da dukiyoyinsu



Duk lokacin da kake tunani zakana tuna abubuwa kala kala da yake faruwa a wannan duniyar wani ya baka mamaki wani ya baka dariya wani ma sai ya baka haushi, wani lokacin zakaga mutane masu hankali wani lokacin kuma sai kaga wasu sun aikata wani abu wanda yai kololuwa a wajen hauka da rashin hankali.

Abubuwa masu yawa kuma kala kala suna faruwa a cikin duniyar nan tamu wanda haka kawai in wani ya aikata a gabanka ko kaji labarin ya aikata sai abin ya baka mamaki harma yasa ka zauna kai kadai kana tunani abinda sukai sai kaga kamar sun fita ne daga cikin hankalinsu ko kuma kai tsaye ace sun haukace ko kuma dai wani abu ne ya same su mai kama da haka.

Wasu daga cikin arnan africa sukanyi banzan tunani wanda har suke tunanin in mutum ya mutu kawai aljanna zai tafi kai tsaye, dan haka mutum zai bukaci kayansa da yake dasu domin yayi rayuwa mai inganci acan koda ya mutu hakan yasa suke tattara duk wani arziki ko dukiyarsu suce in sun mutu a binne su dasu.

Dan haka yanzu zamu kawo muku jerin gidadawan mutanen da aka binne su da dukiyoyinsu.

Gasu kamar haka:-

√ Mutum na farko sunansa yankee shine wanda aka binne shi cikin wata motarsa wanda yafi so da kauna.



√ Sai kuma mutum na biyu wanda shima dai cikin wata hummer jeep dinsa aka binne shi.



√ Bincike ya nuna mutum na uku shine wanda aka yi masa kabarinsa kamar daki sannan aka tsara dakin da ado asaka tv da gado da sauran kayan kida sannan aka binne shi a ciki.



√ Sai mutum na hudu wani dan kasar Uganda ne wanda shi da kudi aka binne shi masu yawa na ban mamaki.



√ Mutum na biyar kuma shima a cikin motarsa mai tsananin kyau da tsada aka binne shi.



√ Sai kuma na shida shima dai daki akai masa mai kyau aka saka shi a ciki wai a cewarsu zai tashi.



√ Sai mutum na bakwai cikin binciken da mukai wanda aka binne shi cikin wata sabuwar MBW.



Wadannan sune jerin mutane bakwai din da aka binne su da wasu abubuwa bayan sun mutu.

-Duniyar labari taku ce.


Comments