Min menu

Pages

   Matar Manya


Manyan labarai masu zafi

Kada kuci wadannan kalar abincin idan har kuna jin yunwa

Nura m Inuwa ya fadi sunayen sabin albums dinsa

Munanan abubuwa guda shida da zasu faru idan aka sare bishiyoyi

                Kashi na farko

Nai tsalle na kauce daga kamun da ta kawomin ban bari shanyayyen hannun nata ya taba jikina ba.

"au nima kake gudu kenan ko abdul?"

safiyyat dake zaune akan keken guragun ta tambaya


Na dubi mummunar fuskarta mai kamar an doki kashi da sanda cikin mamaki sannan nace wai yanzu ke kina nufin kicemin kece safiyan da naketa famar waya da ita nake kin bacci idan dare yayi muke yin waya dake har kike cemin ke Matar manya ce?


Eh nice mana abdul wacce ake yiwa lakabi da MATAR MANYA ko banyi maka bane ta fada lokaci guda kuma ta zaro wata kwalba wadda ga dukkan alamu kayan maye ne a ciki ta daga kwalbar gamida kora ruwan dake ciki sannan lokaci guda ta sake gunguro da keken da take zaune a kai zuwa gareni, ta sake kawo hannun nata mai kamar an jika tsumma da niyyar ta dafani dashi, nai tsalle na kauce a karo na biyu sannan na kalli fuskarta mai kama da goggon biri saboda muni, nai saurin kawar da kaina daga gareta sakamakon hada idon da nayi da jajayen idanunta nai sauri naja da baya lalle kuwa MATA MANYA nace kidime.


Dariya naga tayi hakan shine ya baiwa idanuna damar ganin munanan hakoranta,lokaci guda ta bata rai hakan shine yasa fuskar tata ta sake muni fiye da da, ta fara magana kamar yar maye tace wallahi ok har wani mamaki kake ko dan kaji nace dakai ni MATAR MANYA ce to wallahi bari kaji abdul ko kaki ko kaso saika aureni dan kuwa bazan iya rabuwa dakaiba haka kuma inka tsaya harka batamin rai to kuwa mahaifina a shirye yake da yasa ai maka daurin rai da rai..


Na dubeta daga sama har kasa na kalli shanyayyen hannunta da kuma lamushashshiyarkafarta na sunkuyar da kaina domin nasan ko ana ha maza ha mata bazan taba aurar wannan matar data amsa sunanta da sunan safiya ba...


Farkon labarin

Yammacin ranar ta juma'a yammaci ne dake dauke da dadda dan yanayi wanda ke dadada zuciyar duk wani bil'adama maji dadin zama da kuma rayuwa a cikin daddadan garin..

Wanda hakan shine yasa mazauna garin ke matukar jin dadin zama a daddadar duniyar nan tamu ta mutane..

Sararin samaniya ta zamto mai dadin gani da kuma ban sha'awa kodan ta sanadiyyar kyawawan fararen gajimaren dake ta famar yawo a sararin samaniyar, wadannan abubuwanne ya tilastawa rana dushashewar haskenta sakamakon rufetan da gajimare sukayi hakan yasa garin yin lumshi duk da dai lokacin faduwarta baiyiba..

Cikin garin ya kara kyau fiye da kullum, ko ina ka duba mutanene keta harkokin gabansu wasu na wucewa a babura gamida motoci inda wasu kuwa suke tafiya da kafafunsu ba ruwan kowa da kowa..

Yan mata gamida samari sunyi reras akan manyan titunan dake cikin garin wasu da dama ziyara suka kaiwa yan uwansu dake unguwanni daban daban inda wasu kuma shakatawa kawai suka fito yi tare da kaiwa manyan wuraren dake cikin garin ziyara...

Nima ina daya daga cikin mutanen da suka fito domin kaiwa yan'uwa da abokan arziki ziyara nida kanwata liliane muna tafiya muna maganganu irin na yaya da kanwa babu abinda yasha mana kai..

Karar wayar dake cikin aljihuna itace tai sanadiyyar tsayawata daga tafiyar da nake, nai sauri na zaro da wayar dan ganin waye ke kirana a irin wannan lokacin, banyi wani mamakiba da naga bakuwar numberce dan kuwa inda sabo na riga na saba da irin wadannan kiraye kirayen...

Da irin wadannan kiraye kirayen, nai sauri na kara wayar a kunnena tun kafin nayi magana naji wata zazzakar murya mai dadin sauraro ta fara yimin magana, nai sauri na daidaita bakina sannan na amsa sallamar da tamin lokaci guda kuma nai shiru ina mai jira da sauraron maganar da zata fadamin...

Dan Allah malam mai wayar nake nema idan bazaka damuba zanso ka mika mata kace safiyace ke magana...

Nai shiru bance da ita komai ba saboda tsananin mamakin maganarda naji agun matar data kira sunanta da safiya ta fada, dan nidai na sani wayata ce bata kowa ba to amma gashi wata daban ta kirani kuma har tana cewa na kaiwa mai wayar..

Malam kayi shiru taimaka ka kai mata wayar mana jiranka fa nake ko bakasan kudina ake jaba? Ta tambayeni cikin zafin rai...

Kiyi hakuri hajiya wannan ba number wacce kike nema kika kiraba dan kuwa number tace halak malak sai dai ki duba watakila kin samu matsalane lokacinda kike kokarin saka number nace da ita da sassanyar murya..

Malam gaskiya nikam ban samu wata matsala ba dan daidai nasa number sai dai ban saniba ko kaima kana daya daga cikin barayin waya wanda suke sace wayar mutum kuma suci gaba dayin amfani da layin mutum safiyan ta fada lokaci guda kuma ta katse kiran nata...

Nai saurin duban fuskar wayar tawa gamida fara sallallami cikin mamaki da al'ajabin maganar da wannan matar data kirani tace dani...

Meya farune yaya abdul? Liliane dake tsaye ta tambayeni lokacinda taga alamun mamaki ya baiyana a fuskata...

Uhm karki damu kanwata ba wani abu daya faru kawai dai watace ta kirani kuma sai take cemin wai ba numberta bace ta wata kawar tace, harma take kirana da barawo wanda ya saci wayar kawarta kuma yake amfani da layinta, nayi iya bakin kokarina akan ta fahimceni cewar sai dai in matsala aka samu batasa number daidai ba amma sam taki yarda da batuna...

To kuma menene abin damuwa anan yaya tun da dai ka sani ba satar wayar ko kuma layin kayiba liliane ta fadamin lokacinda ta kuramin ido kamar me kokarin gano abinda ke fuskata...

Ai abinne da mamaki liliane nace da kanwartawa a takaice lokacinda muka kawo kofar gidan da mukeso mu shiga...

Mun jima a gidan yayar tamu muna shira sannan mukayi sallama muka nufi gida kasancewar lokacin sallar magrib yayi hakane yasa ban tsaya munyi shiraba nida kanwata liliane tun lokacinda muka shigo gidan namu, na nufi bangarena domin nayi alwala na karasa masallacin dake kusa da gidan namu...

Zanci gaba a kashi na biyu nine naku Abdulraheem



Comments