Min menu

Pages

Kalli abinda shugaban kasar America yace zai yiwa dukkan musulmin Duniyar nan

 Kalli abinda shugaban kasar America yace zai yiwa dukkan musulmin Duniyar nan


Sabin labarai

Waye shugaban kasar America?


Addinin musulunci da kuma addinin kirista sune manya manyan addinai da ake dasu a duniyar nan a halin yanzu. To amma kuma ana samun yar tangarda da kuma yawan fadace fadace tsakani, inda wani lokacin sai ana yawan samun rashin sasanto walau cikin addinin ko kuma tsakanin addinan guda biyu.

Wasu daga cikin shugabannin america da akayi sukan dauki alkawuran sasanto tsakanin addinan domin suga an daidaita komai kowa yayi rayuwarsa cikin aminci ba tare da fadace fadace ba.

A baya tsohon shugaban kasar America Donald Trump shi hana kusan dukkan musulmin Duniyar yayi shiga kasar sa saboda rashin adalci irin nasa, wannan yasa ya samu yawan suka daga bakin musulmi na kasashe da dama.

To amma wannan sabon shugaban kasar Biden lokacin yakin neman zabensa na shugaban kasa ya dauki alkawarin cewa zai karya wannan dokar daga ranar da yaci kuma aka rantsar dashi ya shiga aiki domin ya sani akwai mafiya yawan na mutane cikin kasar sannan akwai masu yawa da suke shiga a cewarsa.

Sannan yace ai kowa cikin mutane an bashi dama da zai gabatar da al'ada da kuma addininsa dan haka baiga wani dalili da zaisa a zabi wasu al'uma ace za'a hanasu shiga ko kuma gabatar da addinisu a kasar ba.

Dan haka muke da hujja mai karfi cewar wannan shugaban kasar yanada kuduri mai kyau akan dukkan musulmin Duniyar domin tun lokacinda aka rantsar dashi yayi kokari ya canja abubuwa masu yawa wanda tsohon shugaban kasar ya tsara daga ciki harda bada damar shiga kasar ga yan Nijeriya.

Dan haka kowa yanada damar yin comments dinsa domin isar da sakon da yake son isarwa.

Comments