Min menu

Pages

Masoyan Nura m Inuwa sun fito wani abu mai kama da zanga zanga

 Masoyan Nura m Inuwa sun fito wani abu mai kama da zanga zangaA dazu ne muka tsinci photunan wasu daga cikin masoyan gwarzo kuma fitaccen mawakin nan Nura m Inuwa suna zanga zangar cewa ya fitar musu da album din wakarsa da yai musu alkawarin zai fitar musu a wannan shekarar.

Wanda masoyan nasa ke cewa tunda shekarar tazo ya kamata ace ya fitar musu da album din.Mawakin Nura m Inuwa dai ya nuna jin dadinsa matuka ganin wannan tsantsar kaunar da mutane ke nuna masa da har suke yin zanga zanga domin ganin yayi musu, a wani bangaren kuma mawakin ya wallafa a shafinsa na facebook cewa wannan zanga zangar ta zaburar dashi matuka kuma ta nuna masa cewa masoyansa suna tare dashi a koda yaushe.Daga karshe mawakin ya bewa masoyansa hakuri sannan yace kusan koda yaushe da tunanin fitar da wannan album din yake kwana yake tashi bashi da wani buri face ganin yayi abinda zai burgesu. Dan haka yake neman addu'a daga gare su tare da cewa album dinsa yana nan tafe.

Nura m Inuwa dai mawaki ne mai tashe wanda tauraruwarsa ke haskawa tsawon lokaci, hakan yasa ya samu tarin masoya daga kasa Nigeria zuwa ga sauran kasashen duniya. Ya fitar da wakoki na soyayya masu matukar dadi da debe kewa wanda hakan yasa masoya maza da mata kan rububin jin wakokinsa.

Nura m Inuwa shine mutum na farko dana sani da masoyansa ke yin zanga zanga domin ganin ya fitar musu da wakokinsa hakika Allah shine ke daukaka mutum.Duniyar labari taku ce.


Comments