Min menu

Pages

Gwamnan jihar kano ya shirya wata zazzafar muqabula tsakanin malaman Kano da kuma Abduljabar sannan ta fadi sunan malaman da za suyi muqabular

 Gwamnan jihar kano ya shirya wata zazzafar muqabula tsakanin malaman Kano da kuma Abduljabar sannan ta fadi sunan malaman da za suyi muqabular
Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Ganduje ya sanar da shirya wata muqabula tsakanin malaman addini da kuma Abduljabar, hakan ya biyo bayan wata ganawa da gwamnan yayi da malaman addinin kamar yadda wata sanarwa ta kawo.

Abduljabar wani mutumine daya fito a yan kwanakin nan yana wasu maganganu wanda suka saba dokar addini hakan yasa aka rufe wasu gurare nasa.

To amma anji ya fito yana cewa wai ba'a kyauta masa ba.

Ga jerin malaman da za suyi muqabular dashi daga bangarori mabambanta

Daga bangaren izalah

√ Mal Abdullahi sale pakistan

√ Mal sani umar rijiyar lemon

√ Mal abdulwahab Abdullahi gadon kaga

√ Mal Bashir Ali Umar alfurqan

Daga bangaren Qadiriyya/salafiyyah

• Mal Qaribullah labarai

• Mal Mustapha labarai

Daga bangaren Tijjaniyya

✓ Mal Ibrahim shehi mai hula

✓ Mal Nasir Adam Nasir

✓ Mal Bashir Tijjani Usman

Da kuma sauran malamai inda gwamnatin ta ware sati biyu domin su tunkareshi


Comments