Min menu

Pages

Abinda ya kamata ku sani akan kasar Nijar (tarihin duniya)

Abinda ya kamata ku sani akan kasar Nijar (tarihin duniya)


Cikin shirinmu na tarihin duniya yau muna tafe muku da tarihin kasar nijar

Kasar Nijar



A cikin kasashen africa niger na daga cikin kasa data samo sunanta ne daga kogin niger duk kuwa da cewa bata kusa da wata babbar mashigar ruwa, nijar na makotaka da Nigeria da kuma Benin ta kudanci, burkina faso da mali ta yammaci yayinda algeria da libya suke ta arewaci. Sai kuma kasar chadi da take makotaka da ita ta bangaren gabas.

Koda yake sai a cikin karni na sha takwas ne turawa irinsu mango fack dan kasar burtaniya suka fara shiga can bangaren kogin niger to amma dai tun kafin zuwan wancan lokacin faransa take ta kokarin ganin ta mallaki nijar, inda ta samu nasara a shekarar 1890. A wannan lokacin faransa tanada gwamnonin dake tafiyar da harkokin duk kan in yankunan data mamaye a yammacin africa ciki kuwa harda nijar. Wadanda ke aiki a karkashin babban gwamna, wanda ke zaune a dakar na kasar senegal. Ranar goma sha takwas na disambar shekarar dubu daya da dari tara da hamsin da takwas 1958 kasar nijar ta zamto janhuriya mai cin gashin kanta, a karkashin ikon kasar faransa, sannan a ranar uku ga watan disambar shekarar dubu daya da dari tara da sittin 1960 kasar nijar ta samu yancin kai wato shekaru sittin kenan da suka fice.

Nijar tana daya daga cikin kungiyar tallatin arzikin kasashen yammacin Africa wato sidiyawo. Nijar tanada kabilu daban dabam kamar irinsu hausawa zabarmawa bugaje kanuri da larabawa da kuma fulani da kuma bugawa, yarukan kuma sun hadar da faransawa, hausawa, tubawa,kanuri,fillanci, da kuma larabci tamajak zabarmanci dadai sauransu.

A wani bangaren nijar tana da albarkatun ma'adinai cikin kasa kamar irin su zinare, gawayi, karfe, da kuma uranium da kuma fetir.

Gabannin samun yancin kasar nijar an kasa kasar nijar cikin yankunan mulki guda goma sha shida 16 wadanda suka hada da agadez zinder niamey tahoa bilingi diffa,magarya, terra, inguimi, tilleberi da kuma dosso.

Bayan da nijar ta samu yancin kai a shekarar dubu daya da dari tara da sittin an kafa dokar tsara yankuna a watan disambar shekarar dubu daya da dari tara da sittin da daya ta kirkiro da wasu yankuna guda talatin da daya. A wannan lokacin yankunan mulki da ake dasu sunci gaba da kasancewa.

A watan ogustar shekarar dubu daya da dari tara da sittin da hudu dokar tsara yankuna ta sake kasafta nijar zuwa yankuna guda bakwai inda suka hada da agadez,diffa,dosso,maradi, zinder tahoa sai kuma niamey da yake a matsayin babban birnin kasar. An rarraba wadannan yankuna bakwai zuwa gundumomi talatin da shida 36 wadanda su kuma aka sake rarraba su zuwa kananan kauyuka daban daban.

A shekarar dubu biyu da shida 2006 nijar nada kananan kauyuka wanda magadan gari ke shugabanta har dari biyu da sittin da biyar.



Yankin agadez ya hada da hamadar tenere da bilma da kuma yankin eya wadda take cike da tsaunuka. Mafi yawancin jama'ar yankin abzinawa ne akwai kuma hausawa tubawa da fulani.

A yankin Diffa kuma wacce ke iyaka da yankin agadez ta arewa ci da zender ta yammaci da nijeriya ta kudanci sai kuma chadi ta gabashi. Yankin diffa ya kasance daya daga cikin yankuna wanda basu da jama'a sosai wadda kidayar shekara ta dubu biyu da daya wadda ta nuna yawan mutanen yankin ya kusa dubu dari hudu, jama'ar mutanen yankin sun hadar da hausawa da fulani tubawa kanuri, fulani da kuma larabawa.

Bangaren yankin Dosso kuma, an kasa yankin dosso zuwa jahohi biyar da suka hada da boboi, dogon dauchi da dosso da gayah da kuma doga. Yankin dosso na iyaka da jihar sokoto da kuma kebbi na nijeriya a bangaren kudu maso gabas da jihar alibori ta kasar benin ta kudanci. A cikin gida kuma yankin dosso na iyaka da yankin tahoa ta arewa maso gabas da kuma yankunan teleberi da niamey ta yammaci,babbar sana'ar mutanen yankin itace noma.

A bangaren maradi kuma, maradi tana iyaka da Nigeria kidayar shekara ta nuna maradi shine yanki mafi yawan jama'a wadanda yawancinsu hausawa ne, akan yiwa maradi kirari da cibiyar ciyarda kasa saboda harkokin kasuwanci da kuma noman da ake yi a yankin, mafi yawancin abubuwan da ake nomawa a yankin na cikin gida da kuma fitarwa dasu sun hadar da gyada da hatsi da kuma gujjiya koda yake a wasu bangaren akan noma taba da mangoro da alkama da waken suya kai har dama auduga.

A bangaren yankin tahoa kuma mutanen yankin sun kasance hausawa da auzunawa da adarawa da larabawa kuma. Babbar sana'ar mutanen yankin itace noma da kiwo. Yankin tahoa na makotaka ta kudanci da jihar sokoto da yankin gawo na kasar mali ta yammaci da kuma yankin kidal na kasar ta mali ta arewa maso yammaci.

Yankin zinder ko kuma damagaran kabilun dake zaune a yankin sun hadar da hausawa fulani kanuri tare da abzinawa har zuwa shekarar dubu daya da dari tara da ashirin da shida 1926. Birnin zinder shine babban birnin kasar nijar, yawancin tattalin arzikin zinder ya ta'allakane akan noma da kiwo da kuma kasuwanci.

A bangaren telliberi kuma a shekarar dubu daya da dari tara da casa'in da biyu 1992 aka kirkiro yankin na telliberi lokacin da aka raba yankin niamey, yawancin mazauna yankin telliberi zabarmawa ne, wanda sana'ar su itace noma da kiyo. Telliberi shine yanki kadai dake makotaka da yankin Burkina faso kuma yake iyaka da yankin seddo da yaga ta kudu maso yammaci da komando jari.

Niamey kuma shine babban birnin kasar nijar kuma shine birni mafi girma da tsaruwa a kasar, tun a karni na sha takwas aka kirkiro niamey saidai a wancan lokacin ba'a daukeshi da wani mahimmanci ba har sai bayan da faransa ta kafa cibiyarta a wajen a shekarar dubu daya da dari takwas da casa'in. Shekarar dubu daya da dari tara da ashirin da shida ya zama babban birnin kasar ta nijar,sannu a hankali jama'ar mutanen yankin yaita karuwa

Babban musabbin karuwar jama'ar mutanen yankin shine saboda kaurar da akai tayi lokacin fari. Sannan akwai wuraren tarihi wanda suka hadar da gidajen tarihi da kuma gidajen zoo akwai kuma cibiyoyin nuna al'adun gargajiya na america da faransa, sannan akwai manyan kasuwanni guda bakwai a garin. Kaso casa'in cikin dari na mutanen garin musulmai ne.

Domin ganin cikakken bidiyon saiku shiga nan



Comments

2 comments
Post a Comment
  1. ASSALAMU alekum dan owa sunana TANIMU1 TV inada bukatar website approval mai ads nasiyarwa plea

    ReplyDelete

Post a Comment