Min menu

Pages

Akwai yiwuwar mutanen karkara Dana birni a arewacin Nijeriya zasu iya arziki idan sukabi wannan hanya a shekara uku kacal


Akwai yiwuwar mutanen karkara Dana birni a arewacin  Nijeriya zasu iya arziki idan sukabi wannan hanya a shekara uku kacal
 

Akwai yiwuwar mutanen karkara Dana birni a arewacin  Nijeriya zasu iya arziki idan sukabi wannan hanya a shekara uku kacal.

Wannan gida na duniyar labari sashen kasuwanci ya zakulo muku wata hanya gangaran da zata taimakawa mutanen karkara harma dana birni a Najeriya wajen zama masu kudi a shekara uku kacal. Abune budadde a idon kowa cewa mutanen dake karkara a arewacin Najeriya sunfi maida hankalinsu wajen yin noma da kiwo, amma hakan baisa sun kurewa karancin sulalla gudu ba. Rashin taki,rashin kayan aiki, rashin kudi, rashin ishashshan filin noma irin wadannan sune yawancin korafe-korafen manoma.

Abin da duniyar labari ta samo muku a sakamakon bincikenta shine sabuwar fasahar kiwon awaki. Abin zai zama kamar abin dariya ga wasu abin mamaki kuma ga wasu, saboda maimakon suji ance wani abu mai kama da boko sai sukaji ance awaki sune abin da binciken ya gano. Gaskiyane idan mutumin karkara baiyi noma ba to kuwa dole yayi kiwo domin ya rayu a Inda yake, haka kuma wanda ma baya nomanan dogaronsa ta fuskar abinci a wajen makiyaya da manoma yake saboda haka ya zama dole mu rike su sosai, abin farin cikina anan ma shine dayake yawancin mutanan karkarar nada filin gona nasu  na kansu da zasu iya amfani dashi cikin wannan kiwo wanda zai kawo musu kudi da kuma takin da zasu noma abincin da zasu ci.

 Kusan dukkanin manoman karkara kan iya samar da abincin da dabbobi masu yawa zasuci a  shekara daga yayin abin da suka noma(kara da ciyawa),amma kuma abin takaici daga cikin wannan yayin kwata-kwata basa samun abincin da zasuci ishashshe a shekarar saboda babu taki a wajen Wanda zai taimaka a samu amfani mai yawa a maimakon haka ma saidai ciyawa ta fito ta kwace wajen domin ita zata iya rayuwa ko babu taki.

 Awaki na daya daga cikin jinsin dabbobin kiwo masu Saurin haihuwa da yaduwa kuma da ya'ya' masu yawa(biyu zuwa bakwai ko takwas), bincike ya nuna cewa kowace akuya zata iya daukar ciki bayan haihuwarta daga wata 4 zuwa 12, ya danganta da irin jinsin akuyar,lafiyarta,kyan abincin da take ci da duk wata kula dake taimakawa dabbobi su girma, anan yawancin awakinmu a wata 6 ko 7 da haihuwa zasu iya daukar ciki matukar suna da cikakkiyar lafiya da kuma koshi, haka kuma akuya zata iya haihuwa bayan wata shida da daukar cikin, a mafi akasarin awaki a haihuwar farko sukan haifi da daya, a ta biyu kuma sukan haifi ya'ya' biyu ko sama da haka.

Idan harka shirya tsaf kanaso kayi kudi daga kiwon akuya to ga bayanin yadda ya kamata kabi wajen kiwon. Kamar yadda kowace Sana'a keda mataki hakama kiwo keda nasa wato karfi-karfi, don haka wani bazai iya da adadin da wani zai iya farawa ba.

 Anan zanyi bayanin fasalin kiwon awaki 12 ne  idan yaso sai mutum ya dauki adadin dayafi masa.

Muhalli

Kamar yadda duk wani mutum Wanda yasan yadda akuya take to yasan tsarin kiwonsu nada bukatar muhalli Wanda zai basu kariya.

 Muhallin dole ya kasance akwai rumfa ta kwano ko kuma ta yayi, a gona budaddiya ko zagayayya da way a ko kuma itatuwa, idan kuma a gari ne ya zama kewayayyan fili sannan shima da bukatar rumfa kowace irice saboda ruwa da kuma zafin rana. Muhallin dabbobi kowane irine da bukatar wajen shan ruwa a kusa.

Sayan dabbobin

Idan harka shiryawa kiwon dabbobi kana da bukatar sayan masu kyau,lafiya da kuma kira sannan shekara ma abar la'akari ce wajen irin kiwonka, dole ne ka tabbatar akuyar a shekare bata taba haihuwaba ko kuma idan ta taba haihuwa bai wuce haihuwa daya ba. Kudin da ake sayar dasu kuma ya danganta da yankinka ko kuma fasalin akuyar.

Abinci

Abincin dabbobin ka zai samu ne daga yayin abin da kake nomawa,amma ka sani dole shima akwai Wanda yafi mahimmanci, anan shawara duk mai kiwon dabbobi dole ya rika noman gyada da kuma wake, domin samun harawar wake da kuma ganyan gyadar (bubbugin gyada) a matsayin abincinsu,a yayin da ya'ya'nsu kuma zaka iya sayarwa ko kaci. Idan kuma makiyayin awakinsa a gona suke kuma da ishashshan ruwa a wajen saiya gyara waje ya shuka irin ciyayi kamar yakuwa su rika fitowa dabbobinsa naci. Idan kuma ta kama sai ka saying abinci a wajen masu sayarwa ka Tara saboda rani ,amma haka zaici kudi sosai.

Ribar kiwon

Kamar yadda mukayi bayani a baya cewa zamuyi bayanin mu akan awaki goma(12). Anan idan  muka dauka kana da awaki goma(12)a cikin su goma mata (10), biyu maza(2). A shekarar farko cikin uku kowace akuya sai tayi ciki bayan wata shida kuma ta haihu (anan manomi kada ya zarme cewa guda goma idan suka haihu dolene yayan duka sukai labari, a'a zasu iya kaiwa kuma za'a iya samun akasin haka domin akwai jarrabawa da cuta koma ayi bari baki daya, don haka muma anan zamu cire guda biyu cikin lissafin mu ko hakan zai iya faruwa),  wato bayan an haifi yaya takwas a madadi goma. 

A cikin takwas din nan sai aka sami uku maza ne, biyar kuma mata ne, wato muna da mata 15 kenan maza kuma 5, a jumlace sun zama 20. Bayan shayarwar Sati uku ko wata guda sai kowace cikin goman nan na farko suka sake maida ciki (tsawon lokacin shayarwa akuya daga sati uku ne zuwa wata uku, don haka idan suna samun isassan abinci mai inganci zasu iya yaye yayansu a sati uku kuma su maida ciki).

 Bayan wata shida sai aka sake samun akuya goman sun sake haihuwa an samu takwas wato maza 3 mata 5, a jumlace ana da awaki 28 a haihuwa sau biyu kawai,adadin mata ya koma 20 maza kuma 8. 

Bayan sunyi reno sun yaye goman nan zasu dauki cikin ne tare da yayansu na farko tunda sunkai sama da wata shida da haihuwa, anan awaki 15 zasu haihu kenan. Bayan sun haihu sai suka haifi yaya 13, daga ciki 4 maza, 9 mata, a jumlace ana da awaki 41 kenan maza 12,mata 29, wannan duk a shekara daya da wata 9 idan aka hada harda watannin reno.
 
Anan idan mukaci gaba da lissafi sai mutum ya gaji da karantawa don haka makiyayi yana dakyau ya sani a shekara uku kacal zasu iya zama guda 57, a yayin da a cikin bayanin banyi batun masu haihuwa bibbiyu ba. Kaga kenan zasu iya ninkawa ma daga adadin dana lissafa bayama idan adadin matan ya wuce na mazan da muka kiyasta. 
Daga karshe kowa ya sani burin mu anan shine kowa ya fita daga kangin talauci ya samu rufin asiri bawai sai mazauni karkaraba harda dan birni kowa nada ikon aiki da wannan tsari@ duniyar labari.
MARUBUCI BASHIR ABDULAZIZ
@duniyarlabari.com

Comments