Min menu

Pages

Dr Ahmad Gumi bai cancanci haka ba a gunku yan arewa

 Dr Ahmad Gumi bai cancanci haka ba a gunku yan arewa


A kama Malam Gumi inji yan Nijeriya

Kasar Nijeriya tafi kowacce kasa mafi yawan matalauta

Yar Atiku tayi rijistarta da jam'iyar Apc

Hakika Malam Ahmad Gumi ko kusa bai dace kumar haka ba yan arewa.


Domin idan baku yabe shi tare da gode masa ba ko kadan bai kamata har kuna cewa haka a kansa ba.


Wasu mutane sunada abin mamaki ko kuma abin haushi da har suke iya fadar wata magana wadda bata da kan gado amma in ba haka ba ta yaya har wasu za suna cewa wai a kama Malam.


Lokacin da naji ana fadar hakan har mamaki nayi da wai dan Nijeriya ne kuma dan arewa shine ke cewa a kama Malam Gumi mutumin da a dalilinsa an samu yan bindinga sun saki mutane babu adadi.


A dalilinsa yan bindinga da yawa sun tuba.


A dalilinsa yan ta'adda masu yawa sun ajiye makamansu

Ta dalilinsa yan bindiga da dama suka shiryu.


Shine mutum daya da ya saida ransa da rayuwarsa yake shiga kungurumin jeji domin zama da yan bindingar da suka dauke mana mutane.


Shine yake iya hakura da rayuwarsa ya tunkari jejin da babu masu iya shiga ya shiga ya nemi sulhu da yan bindingar harma su aminta dashi nasihar da yake musu tasa su saduda su saki mutanen da suka kama.


Wanda badan ya shiga jejin ba da tuni wasu da dama sun mutu da har yanzu wasu basu koma gidajen su ba.


Amma abin mamaki yau mutumin da yake wannan fadi tashin ne wasu ke cewa a kama shi saboda ba dan akidarsu bane.


Ba dan kungiyar su bane, ko kuma yayi abinda suka kasa.


Banda malam din waye ya saida rayuwarsa ya shiga wannan jejin? 

To ana adalci gaskiya cikin duk wasu abubuwa da muke yana da kyau muna fadar magana mai kyau ga duk wani musulmi koda ba dan kungiyar mu bane

Comments