Min menu

Pages

A kama da Dr Ahmad Gumi Inji Yan Nigeria

 

Wasu 'yan Najeriya sun bayyana ra'ayinsu kan da'awar Gumi na shiga daji wajen 'yan bindiga - Sun nemi gwamnati ta gaggauta kama malamin tare da yi masa tambayoyi kan mafakar 'yan bindiga - Hakazalika wasu suna ganin malamin yana da kyakkyawar masaniya dagane da inda 'yan bindigan suke '

Malam Gumi bai cancanci haka ba

Yan Najeriya a shafukan sada zumunta sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ba da umarnin kama Malamin  da bincikensa


 shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, kan mu'amalarsa da 'yan bindiga a kasar, The Punch ta ruwaito. A baya, an ga Sheikh Gumi a cikin hotuna yana tattaunawa da wasu gungun 'yan bindiga a dazukan Zamfara, Neja da sauran jihohi. Ya kuma bayar da shawarar a yi afuwa ga 'yan fashi kamar yadda aka yi wa' yan bindiga a yankin Neja Delta. Mun ruwaito cewa, Sheikh Gumi, a ranar Litinin, ya ce 'yan bindigar sun kashe mutane "kalilan" ne kawai cikin rashin sani, ya kara da cewa sun kashe ne don "ramuwar gayya". Kalaman Sheikh Gumi na baya-bayan nan sun ja hankali a shafukan sada zumunta inda yawancin masu amfani dasu suka bayyana shi a matsayin kakakin 'yan bindiga a kasar. 

Hakanan, wasu masu amfani da Facebook ba su ji dadin maganganun da ayyukan malamin na baya-bayan nan ba, suna kira ga hukumomin tsaro da su kamo shi nan take don amsa tambayoyi. 


Zauren fiqhus sunnah
Zauren fiqhus sunnah
BARKA DA ZUWA WEBSITE DINMU NA-- DUNIYAR LABARAI MUNA SANAR DA MASU SHIGA WANNAN SHAFI CEWA ZAMU CIGABA DA FADAKARWA ,DA ILMANTARWA INSHA-ALLAH Phone Number 08084396103 Email Zaurenfiqhussunah@gmail.com

Comments