Min menu

Pages

Nijeriya ce kasa mafi yawan matalauta inji Nasiru El-rufa'i

 Nijeriya ce kasa mafi yawan matalauta inji Nasiru El-rufa'iGwamna mai ci na Kaduna ya siffanta kasar Nijeriya a matsayin kasa mafi tarin matalauta.


Ya fadi haka ne yayin wani taro na kula tare da kare rayukan mutane da suka gabatar a Kaduna.


Gwamnan yace Nijeriya tana cikin wani hali wanda take sahun farko a yawan matalauta a duniya.


A wani bangaren yace ya kamata masu mulki da kuma masu kudi suna taimakawa mutanen da basu dashi domin a kori talaucin da yai katutu a kasa.


Bayan nan kuma gwamnan ya gabatar da wani shiri na taimakawa masu karamin karfi a jihar ta Kaduna.

Comments