Min menu

Pages

 YAR ATIKU TAYI REGISTA DA JAM'IYAR  APC


Yan Nijeriya suna cewa a kama Malam Gumi

Ya' ga tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyar PDP a 2019 Atiku Abubakar ta sabunta katinta Na jam'iyar APC a Jahar Adamawa.

Ya' ga mai suna Fatima mai shekaru 49 Wanda tsohuwar kwamishinar lafiya ce a jahar Adamawa a zamanin gwamnatin jibrilla bindow ta sabunta katinta na jam'iyar APC. Fatima tayi rigista a gunduma ta daya mazaba ta 08 dake a karamar hukumar Jada ta jahar Adamawa.

Mista Ibrahim bilar shugaban jam'iyar APC a jahar Adamawa ya tabbatar da sabunta rigistar.

Fatima abaya tace bata bi mahaifin nata ba zuwa PDP.

Atiku Abubakar dai na zama daya daga cikin jigogin PDP a Najeriya Wanda har yayi takarar neman shugabancin kasa a cikin ta, abisa kasancewarsa jigo a PDP kuma yarsa ma bata tare dashi shin makomar siyasar atiku kuwa batayi rauni ba?

Duba da halin da ake ciki na matsalolin siyasa ana ganin shugaba Atiku zai iya sake neman Takara a zabe mai zuwa a yayin da kuma abubuwan siyasa keta canjawa alkiblar siyasarsa fasali jama'a da dama na ganin Atiku sai yayi da gaske wajen sake zage damtse matukar yana son yin takara a shekarar 2023.

Comments