Min menu

Pages

Apc sai tayi shekara fiye da dari tana mulki inji wani dan majalisa


 Apc sai tayi shekara fiye da dari tana mulki inji wani dan majalisa

Matar Manya

Apc zatai fin shekara dari tana mulki inji wani dan siyasa dake wakiltar pankshin/kanke/kanam Yusuf Gagdi.

Yace jam'iyar nada damar yin shekaru fin dari tana mulki idan har zata ci gaba da gabatar da irin wadannan aiyukan na raya kasa da kuma tallafawa matasa da mata harma da tsofaffi.

Ya fadi maganar ne lokacinda yaje sake tabbatar da register sa ta zama dan jam'iyar a gum gagdi a karamar hukumar kanam, a jihar Plateau.

A cewarsa jam'iyar nata kara girma tun shekarar dubu biyu da goma sha biyar data karbi mulki.

Sannan yace jam'iyar na gabatar da abubuwan alkhairi wanda zaisa su kuma zabarta duk adadin shekarun da za tayi.

Duba da yanda mutane keta rububin shiga jam'iyar.


Comments