Min menu

Pages

Yanda zaka haddace Alqur'ani mai girma da wannan App ɗin cikin sauƙi

YANDA ZAKA HADDACE ALQUR'ANI MAI GIRMA CIKIN SAUƘI

Assalamu alaikum warahmatullahi ƴan uwa barkanmu da wannan lokaci sannan kuma barkanmu da sake saduwa a wannan sabon darasin.

Acigaba da kawo muku muhimman Applications da wannan channel take a yau darasin namu zeyi duba ne izuwa wata manhaja me matuƙar amfani wadda zata koya maka yanda zaka haddace Alqur'ani mai girma cikin sauƙi.

DALILIN KAWO WANNAN MANHAJA

Kaso me matuƙar yawa na matasanmu dama al'umma suna san haddace Alqur'ani mai girma sedai a sau dayawa sukan samu gazawa ta hanyar kasa gane wani salo ya kamata subi domin kiyaye wannan haddar idan an haddace ta. Ta inda zakaga ɗalibai sukan nemi malamai ko kuma abokan karatunsu wanda ze dinga tayasu jin wannan haddar tasu shin dai-dai ne ko kuma akwai kuskure, to wannan gaskiya yana bada wahala wajan saka mutum ya dinga maka wannan aikin, a don haka muka zaƙulo mana wannan App din wanda ze taimaka mana wajan maye gurbin wanda zasu kular mana da haddarmu ta Alqur'ani mai girma.

NASAN ƳAN UWA ZASUCE YA AKE AIKI DA WANNAN ALQUR'ANIN ME SUNA TARTEEL?

Da farko bayan ka sauke shi a cikin wayarka kagama saka masa duk wani settings kawai abu na fari da ze nuna maka shine surori na cikin Alqur'ani wanda babban aikinsa ze baka dama ka karanta Sura idan kai kuskure kai tsaye zakaga ya tsaya ya saka maka alamar cewa inda fa ka biya ɗin nan ba dai dai bane kaje ka sake dubawa domin gyara kuskuren naka. A cikin wannan Alqur'ani mai girma akwai abubuwa da yawa wanda munyi bayani a bidiyon da muka saka muku a channel ɗin, da zaran ka sauke shi zaka koyi wasu ƙarin abubuwa wanda lokaci baze barmu muyi bayanin komai da komai ba.

Idana kanasan Sauke wannan Alqur'anin mai girma kuma me kyau danna NAN

da zaran ka danna ze kaika Google Playstore wanda zakaga wani waje da aka rubuta Install kana dannawa ze sauka a wayarka kawai zaka fara amfani dashi cikin sauƙi.

Idan wannan darasin ya burgeka zaka iya masa Like sannan kai mana share domi  ƴan uwa su gani su amfana

Wasalam alaikum

mun gode.

Comments

2 comments
Post a Comment

Post a Comment