Min menu

Pages

Yanda zaka raba sauti dabam waƙa dabam

Assalamu alaikum warahmatullahi ƴan uwa barkanmu da wannan lokaci sannan kuma barkanmu da sake saduwa a wannan sabon darasin.


A cigaba da kawo muku muhimman Application da wannan channel take a yau munzo muku da wani App guda ɗaya tilo wanda munada tabbacin ze burgemu sannan kuma zamuyi amfani dashi koda a nan gaba ne, domin kuwan wannan App ɗin ba kasafai muka fiya haɗuwa da irinsu ba.DALILIN KAWO WANNAN APP ( MOISES)

Wannan manhaja me suna a sama nasan dayawan mutane sun jima suna jirana samun irinta domin wataran kawai zaka wayi gari kaji kana da buƙatar jin waƙoƙin gargajiya kawai bayare da kiɗaɗe ba. Ko kuma a gefe guda zakaji kanasan jin kiɗe kiɗen batare da jin waƙoƙin da ake faɗi ba, ta yiwu baka fahimtar yaran da ake rera waƙar dashi amma kiɗan waƙar yana burge ka. Adon haka mulazo da bayanin wannan Manhaja wanda ze baka damar cire waƙa ko kuma cire sauti shi guda tilo batare da ka sha wahala ba wanda baze ɗaukar maka mintina uku ba zaka gama tsaf.


YAYA AKE AMFANI DA WANNAN APP ƊIN?


Bayan ka sauke wannan Manhaja kawai zakaga wakan Next seka dinga dannawa har ya kaika ga inda zakai Select na Email ɗinka zaka zaɓi email ɗin da yake a kana wayarka kawai ka danna, ta yiwu ya tambaye ka kanasan Sabbin Updates akan wannan App ɗin ta cikin Email zaka iya danna "Don't Allow" inkuma kanaso ka danna. Kai tsaye ze nuna maka wata fuska wato inda zaka daɗa wakar da kake so ka cire Sautin ko waƙar kana danna nan wato " Add a song" shikenan ze nuna maka inda zakai adding kodai ta hanyar Gallery  ko Cloud storage ko kuma File app. 


Mu ƙaddara mu bidiyo ma zamu cirewa sauti muna dannawa zakaga yana processing daganan kaga yana downloading duk zaka iya jiransa cikin minti ya gama cire maka wannan bidiyon ya maidashi sauti kawai.. daganan zakaga fuskar da mukai bayanin wannan App ɗin a bidiyon kai tsaye batare da bambanci ba, sekai abunda kake so.


Idan wannan App ɗi  ya burgeka kanasan sauke shi cikin sauƙi Danna NAN

Bayan ka danna ze kaika Google Playstore sekai install daga bisani ka danna Open.


Wa salam alaikum,

mun gode.

Comments

3 comments
Post a Comment

Post a Comment