Min menu

Pages

Yanda zaka kama me bincike maka waya

Yanda zaka Kama me maka bincike a waya

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu ƴan uwa barkanmu da wannan lokaci sannan kuma barkanmu da sake saduwa a wannan sabon darasin, wanda muke koya wasu harkoki da suka shafi Technology na zamani musamman na wayoyin hannu.


A cigaba da kawo mana muhimman Application da wannan channel take a yau munzo muku da wasu Manhajoji guda biyu wanda mukai amfani dasu kuma suka ƙayatar damu sannan muka ga ya kamata ace mun nunawa ƴan uwa domin su dubasu su koye su sannan su saka a wayoyinsu na hannu domin jin daɗinsu.

Menene dalilin kawo wannan App ɗin?

A lokuta da yawa mukan saka wayarmu a caji ko kuma mu ajiye ta a wani waje wanda bamusan kowa ya taɓa ta. Ko kuma ma zaka iya bada aron wayar tare da bada sharaɗin cewa kada wanda ya shigar maka whatsapp ko facebook ko dai wani wajan wanda ze zama sirri a wajanka.A don haka muka yanke shawarar kawo wannan App ɗin wanda ze taimaka maka wajen gano duk inda aka shiga a wayarka ta cikinsa ba tare da wanda kabawa ba ya sani, wani abun burgewa hadda hoton wanda ya ɗauki wayar wannan App ɗin ze nuna maka.

(BAYANIN  APP NA FARKO A TAƘAICE)

Kawai da zaran ka sauke wannan App ɗin daga Google Playstore zaka buɗe shi kana buɗewa ze nuna maka inda zaka saka Password, seka saka.Daga nan zakaga Alamar kashewa da kunnawa a gefen hannunka na dama, a can sama dai a hannunka na dama zaka alamar Settings nanma zaka danna, seka kula zakaga jerin wasu Alamomi seka bude su idan ba'a buɗe suke ba, seka buɗe su duka, daga nan kawai zakai baya ka dannan Alamar kunnawan nan wadda mukai bayani a baya, seka futa daga App ɗinka.

TO YAYA ZAN GANO WANDA YA SHIGA DA HOTONSA?

Kawai ana baka wayarka ko kuma kana ɗaukar wayarka zaka shiga cikin App ɗin daga nan zakaga ya tambaye ka Password ɗinka da ka saka kana sawa, kawai zakaga Report na inda aka shiga da kuma fuskar wanda ya shiga 

Idan kanasan Sauke  wannan App ɗi 

DANNA NAN

BAYANIN APP NA BIYU ( Snap edit)

Wannan App ɗin shima ba sabon App bane a wajan mutane, sedai wannan lokacin an sabunta fuskarsa da kuma abubuwa da dama sabbi da yazo dasu wanda nasan zasu sauƙaƙawa masu amfani dasu sannan kuma zasu burgemu duka a lokaci guda.

YAYA AKE AMFANI DASHI?

Yanada saukin amfani bayan kai installing kana buɗewa kawai zakaga wata alama daga ƙasa a gefen hannunka na dama zakai ta dannawa har kamar sau uku ze ta nuna maka wata fuska daga nan ze kaika wata fuska da zakaga an rubuta maka a turance Start may 3 days free. Kawai ka dannan can sama hannunka na dama alamar Cancel. Kai tsaye ze buɗe maka fuskar da zakai ayyu a cikinsa daga cikin manyan ayyukan sun haɗa da;

1: yanda zaka cire Background na kowani hoto

2: yanda zaka ƙarawa tsohon hotonka clear sosai

3: yanda zakai Editing hotonka yai kyau

4: yanda zaka maida hotonka kamar Cartoon

Ka danna NAN idan kanasan Sauke shi

Bayan ka danna ze kaika Google Playstore se ka danna install daga nan ze sauka a wayarka.

idan wannan darasin ya burgeka muna fatan zaka danna masa Like sannan kai share domin ƴan uwa su gani su amfana.

Wa salam

Mun gode.

Comments

1 comment
Post a Comment

Post a Comment