Min menu

Pages

Makomar: Bellingham, Rice, Mount, Mendy, Szoboszlai, Cancelo, Kimmich, Asensio, Moyes, Nelson

 

Musayar yan wasa a yau Asabar makomar: Bellingham, Rice, Mount, Mendy, Szoboszlai, Cancelo, Kimmich, Asensio, Moyes, Nelson 


Ga Kanun labaran

Madrid na daf da daukar Bellingham, Asensio Kuma zai bar kungiyar inda PSG ta mika tayi, Chelsea ta sawa Mount kudi inda United ke ci gaba da bibiyar Dan wasan, City tayiwa Cancelo kudi Wanda Barcelona keson dauka, Arsenal naci gaba da karbar tayi na Dan wasa Nelson bayan ya sabunta kwantiragi

Ga cikakken labarin 

Real Madrid na shirin daukar dan wasan tsakiyar Ingila Jude Bellingham, mai shekaru 19, daga Borussia Dortmund a mako mai zuwa. (Marca - in Spanish)


Dan wasan tsakiya na West Ham da Ingila Declan Rice zai gwammace ya koma Arsenal a wannan bazarar, inda Manchester United, Chelsea da Bayern Munich suma ke zawarcin dan wasan mai shekaru 24. (Mirror)


Har yanzu Manchester United ba ta kai ga biyan fam miliyan 55 da Chelsea ta yi wa dan wasan tsakiyar Ingila Mason Mount kudi ba duk da cewe itace kan gaba wajen neman dan wasan mai shekaru 24. (Independent)


Chelsea na neman siyar da daya daga cikin masu tsaron ragar kungiyar ta farko, ciki harda dan wasan Senegal Edouard Mendy, mai shekaru 31, mai yuwuwar barin kungiyar a bazara. (90min)


Newcastle ta aike da 'yan kallo don kallon dan wasan tsakiya na RB Leipzig da Hungary Dominik Szoboszlai, mai shekaru 22, sau biyu a makwannin da suka gabata. (Sky Sports)


Manchester City ta sanya farashin Yuro miliyan 40 (£35m) kan dan wasan bayan Portugal Joao Cancelo, wanda a halin yanzu yake zaman aro a Bayern Munich, inda Barcelona ke zawarcin dan wasan mai shekaru 28. (Sport - in Spanish)


City ta shirya yin amfani da Cancelo wajen musayar dan wasan Bayern da Jamus Joshua Kimmich, mai shekaru 28. (90min)


Marco Asensio na shirin barin Real Madrid idan kwantiraginsa ya kare a karshen kakar wasa ta bana bayan tattaunawar kwantiragi tsakanin kungiyar da dan wasan tsakiyar Spain, mai shekaru 27, ya lalace. (Athletic- subscription required)


Asensio yana tattaunawa da Paris St-Germain a matsayin Dan wasan kyauta. (ESPN)


Tottenham ce ke kan gaba wajen neman golan Brentford da Spain David Raya, mai shekaru 27. (GiveMesport)


Golan SC Freiburg da Netherlands Mark Flekken yana gab da rattaba hannu a Brentford, in da kulob din Premier na shirin kunna batun sakin dan wasan mai shekaru 29 €13m (£10.4m). (Sky Sports Germany)


Da wuya Leeds United ta sayi dan wasan tsakiyar Amurka Weston McKennie, mai shekaru 24, na dindindin a wannan bazara da zarar yarjejeniyar aronta daga Juventus ta kare. (Calciomercato - in Italian)


West Ham tana son dan wasan bayan Arsenal Nuno Tavares, mai shekaru 23, wanda a halin yanzu yake zaman aro a Marseille. (Record - in Portuguese)


Kocin Hammers David Moyes ya ce zai duba 'yan wasan Burtaniya da na gida a wannan bazara in da kulob din ake alakanta shi da dan wasan tsakiya na Southampton da Ingila James Ward-Prowse, mai shekaru 28, da kuma dan wasan Leicester da Ingila Harvey Barnes. (Standard)


Dan wasan Arsenal dan kasar Ingila Reiss Nelson, mai shekaru 23, na shirin kulla sabuwar yarjejeniya ta dogon lokaci da kungiyar. (Athletic- subscription required)


Tottenham zata saurari tayin dan wasan bayan Wales Ben Davies, mai shekaru 30 a wannan bazarar. (Football nsider

Comments