Min menu

Pages

 

Musayar yan wasa a yau ranar Juma'a makomar: Kane, Rice, Mount, Rabiot, Lavia, Maddison, Rodgers, Potter, Ugarte, Dalot, Dimaria


Ga kanun labaran

United ta tuntubi Wakilin Rabiot, ka zalika kungiyar na kokarin daukar Rice, Mount da Kane, a wani bangaran Kuma an bawa Madrid damar daukar Kane, PSG ta kai takai tayin Ugarte Wanda itama Chelsea ke zawarcin Dan wasan na Lisbon, West Ham zata day Rodgers ko Potter


Ga cikakken labarin 

Manchester United na son sayen dan wasan gaban Tottenham Harry Kane, mai shekaru 29, da dan wasan tsakiya na West Ham Declan Rice, mai shekaru 24, da kuma dan wasan tsakiya na Chelsea Mason Mount, mai shekaru 24. (Sky Sports)


An bai wa Real Madrid damar sayen kyaftin din Ingila Kane. (Cadena Ser - in Spanish)


Manchester United na neman Mount inda hakan ka isa iya dan wasan tsakiyar Netherlands Donny van de Beek, mai shekaru 26, ya bar Old Trafford a bazara tare da Scott McTominay, inda Newcastle da West Ham suke zawarcin dan wasan tsakiyar Scotland din mai shekaru 26. (Sun)


United ta fara tattaunawa da mahaifiyar kuma wakiliyar dan wasan Juventus da Faransa Adrien Rabiot, da niyyar daukar dan wasan mai shekaru 28 a kyauta. (Nicolo Schira)


Tottenham na la'akari da kocin Celtic na Australia Ange Postecoglou a matsayin dan takarar neman mukamin bayan Arne Slot ya yanke shawarar ci gaba da zama a Feyenoord. (Independent)


Haka kuma Spurs din ta tuntubi tsohon kocin Leicester Brendan Rodgers, da tsohon kocin Chelsea Graham Potter da tsohon kocin Spain Luis Enrique suma suna cikin jerin sunayen 'yan takakar da zasu nema su nada. (Football transfer)


Duk da haka, Enrique shi ma ya fito a matsayin wanda zai maye gurbin kocin Paris St-Germain Christophe Galtier. (Goal)


Chelsea da Liverpool suna sa ido kan dan wasan tsakiyar Belgium Romeo Lavia, mai shekaru 19, amma tsohuwar kungiyarsa Manchester City ba ta cikin Wanda zasu dauko dan wasan tsakiyar Southampton din. (Time - subscription required)


Dan wasan tsakiya na Leicester City da Ingila James Maddison, mai shekaru 26, da dan wasan bayan Arsenal da Scotland Kieran Tierney, mai shekaru 25, su ne manyan ‘yan wasan da Newcastle United zatayi zawarcinsu a wannan bazarar yayin da suke neman karfafa ‘yan wasanta a gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa. (i Sport)


AC Milan ta sanya dan wasan tsakiya na Chelsea da Ingila Ruben Loftus-Cheek, mai shekaru 27, a gaba cikin jerin Yan wasan da zatayi zawarci a wannan bazarar. (Fabrizio Romano)


AC Milan ta tuntubi wakilan dan wasan gaban Liverpool Roberto Firmino da ya bar Liverpool kan yiwuwar daukan dan wasan Brazil mai shekara 31. (Calciomercato - in Italian)


Manchester United na ci gaba da bibiyar dan wasan tsakiyar Leeds United Tyler Adams, mai shekaru 24. Da alama Leeds din ba za ta ci gaba da rike kyaftin din Amurkan ba idan ta bar gasar Premier. (Football Insider)


A kwanakin baya ne Newcastle ta aika yan kallo domin kallon dan wasan tsakiyar RB Leipzig kuma kyaftin din kasar Hungary Dominik Szoboszlai, mai shekaru 22. (Sky Sports)


Fulham na tattaunawa da wakilan dan wasan gaban Brazil Willian don tsawaita zaman dan wasan mai shekaru 34 a Craven Cottage na wani kakar wasan. (Fabrizio Romano)


Everton ta tuntubi kocin Botafogo, Luis Castro, mai shekaru 61, yayin da suke tattaunawa kan maye gurbin Sean Dyche a matsayin koci a bazara. (Daily record)


Paris St-Germain ta kai tayin neman dan wasan tsakiyar Sporting Lisbon da Uruguay Manuel Ugarte, yayin da Chelsea ma ke zawarcin dan wasan mai shekaru 22. (Fabrizio Romano)


Dan wasan gaban Argentina Angel di Maria na shirin barin Juventus a matsayin kyauta a wannan bazarar, inda wasu kungiyoyin MLS da na Saudi Arabiya suke zawarcin dan wasan mai shekaru 35. (90min)


Dan wasan bayan Portugal Diogo Dalot, mai shekaru 24, yana kan matakin karshe na tattaunawa don rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya ta dogon lokaci a Manchester United. (Fabrizio Romano)


PSV Eindhoven ba za ta sayi dan wasan bayan Everton ba Jarrad Branthwaite kan kwantiragin dindindin ba duk da cewa dan wasan mai shekaru 20 ya burge ta a lokacin zaman aro na tsawon kakar wasa. (Football Insider)


Newcastle da Aston Villa na daga cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan tsakiya na Swansea City da Scotland Azeem Abdulai, mai shekaru 20. (Mail)


Yar wasan bayan Spain Ona Batlle, mai shekaru 23, ta amince ta koma Barcelona idan kwantiraginta na Manchester United ya kare a bazara. (90min)


Dan wasan bayan Brazil Rafaelle Souza, mai shekaru 31, zai bar Arsenal a bazarar nan bayan ya shafe watanni 18 a kulob din. (Athletic- subscription required)

Comments