Min menu

Pages

Hasashen wasannin satin nan English Premier League sati na 38

 

Hasashen wasannin sati na 38 English Premier League


Fashin baki

 Duk da an zo ranar karshe akwai sauran yaki ga Everton, Leicester da Leeds domin tsira a gasar. Duk da haka kungiya daya ce kawai zata ci gaba da zama a gasar ta Premier, amma wa zai tsira? Shine abin tambayar.


"Ranar Lahadi za ta kasance mai ban sha'awa," 


"Daukar maki da Leicester tayi a karawar ta da Newcastle a ranar Litinin na iya zama babban sakamako ga kungiyar. Har yanzu suna buƙatar doke West Ham don samun damar zama a gasar, idan sun tsira daga nan, zai iya zama ɗaya daga cikin mafi girman tsira da muka taɓa gani a tarihin gasar wanda bana tsammanin hakan.


"Wannan sakamakon yana nufin Everton ta doke Bournemouth don tabbatar da tsayawa tsayin daka itama a gasar, amma kuma har yanzu Leeds itama tana da dama saboda zasu buga wasa da Tottenham ne da ba su da kyau."


Premier League - mako na 38

Lahadi, 28 ga Mayu    Hasashen 

Arsenal vs Wolves                     3-0

Aston Villa vs Brighton             2-1

Brentford vs Man City               1-2

Chelsea vs Newcastle                0-2

Palace vs Nott Forest                2-0 

Everton vs Bournemouth          2-1

Leeds vs Tottenham                   2-2

Leicester vs West Ham              2-1 

Man Utd vs Fulham                     2-0

Southampton vs Liverpool        0-3


Arsenal vs Wolves

Babu wani abu mai mahimmanci a wannan wasa ga kowane bangare amma Arsenal za ta so ta kammala kakar wasa mai kyau ta hanyar nuna bajinta a gaban magoya bayanta.


Sun rasa damarsu ta lashe gasar a cikin 'yan makonnin nan amma wannan dama ce a gare su domin nuna sun Yi fice tare da kyakkyawan wasa, kuma ina tsammanin abin da za su yi ke nan.


Akwai yar damuwa ga Wolves cewa akwai shakku game da makomar Julen Lopetegui saboda ya yi aiki mai kyau - sun kasance a kasan tebir lokacin da ya karbi ragamar aikin kungiyar a watan Nuwamba. Kungiyar ta su ta yi kyau sosai bayan ya karbeta, amma ana iya samun rani marar tabbas a gaba a Molineux.


Arsenal vs Wolves     3-0


Aston Villa vs Brighton

Tuni dai Brighton ta tashi kunnen doki da Manchester City a ranar Larabar da ta gabata, ta riga ta samu gurin buga gasar Europa kaka mai zuwa, amma har yanzu Aston Villa na da sauran aiki.


Villa dole ne ta nemi dace wa da sakamakon Tottenham a Leeds kuma tayi fatan Brentford ba za ta doke Manchester City ba don samun gurbin shiga gasar Europa conference.


Aston Villa, Tottenham da Brentford duk za su iya kammala gasar a matsayi na bakwai dangane da abin da zai faru a ranar karshe

Villa ta doke Seagulls kafin gasar cin kofin duniya, bayan Unai Emery ya karbi ragamar horas da 'yan wasan, amma ban da tabbacin za su sake samun nasara a bangaren Roberto de Zerbi a wannan karon.


De Zerbi ya yi sauye-sauye a karawar sa da City kuma ya bar Lewis Dunk a benci amma duk da haka ya samu maki a kan zakarun gasar. Watakila zai sake jujjuya tawagarsa, amma har yanzu ban ga sun yi asara ba. Wasan nafi tsammanin za'a iya raba maki, 1-1, amma dole na zabi Wanda zai nasara.


Aston Villa vs Brighton   2-1


Brentford vs Man City

Brentford ta sake samun kyakkyawan yanayi kuma za ta iya kammala wasan biyu da samun nasara a kan Manchester City bayan ta doke su a filin wasa na Etihad a watan Nuwamba.


Mun san yadda kocin City Pep Guardiola ke da burin samun nasara a kowane wasa saboda ya nuna hakan a karawarsu da Brighton, amma ina mamakin ko wasu daga cikin ‘yan wasansa za su buga wasan da idon su daya a kan wasan karshe na cin kofin FA na mako mai zuwa, su kuma yi tunanin wasan karshe na gasar zakarun Turai. .


Har yanzu ina goyon bayan City tai nasara anan, amma zai kasance kusa.


City suna abin da ya kamata - abin da suke yi ya cancanta saboda horarwar da Pep yake musu tana da kyau sosai. Brentford na taka rawar gani sosai a karkashin Thomas Frank kuma Bryan Mbeumo yana cikin yanayi mai kyau don haka za su iya samun nasarar sa kwallon a raga, amma City na da karfin gaske. 


Brentford vs Man City   1-2


Chelsea vs Newcastle

Newcastle na iya kasancewa cikin yanayin jin dadi yanzu saboda suna da tabbacin buga gasar zakarun Turai don haka wannan hasashen wani bangaren sa ya dogara da kwazon su da yanayin farin cikin su.


Manchester United da Newcastle sun samu gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai, yayin da Liverpool da Brighton za su kasance a gasar Europa a kakar wasa mai zuwa.

Duk da haka, har yanzu dole ne ku yi la'akari da yadda Chelsea ba ta da kyau. Sun kasance cikin yanayin bala'i a duka kakar wasa ta bana kuma ƙungiyoyi huɗu na ƙasa su ne kawai waɗanda suka yi nasara a cikin gida kaɗan fiye da su a wannan kakar.


Ba za a sami abubuwa da yawa ba don magoya bayan Chelsea su yi murmushi a Stamford Bridge ba a ranar Lahadi.


Wasan Newcastle da Chelsea kamar mafarauta ne da ke tahowa kan ɗanyen nama.


Chelsea vs Newcastle  0-2


Crystal Palace vs Nottingham Forest

Na san Roy Hodgson yana samun dan kadan amma Crystal Palace ba za ta iya yin gaggawar kawar da shi ba.


Ya yi wani gagarumin aiki tun da aka nada shi a karshen watan Maris, to wa zai shigo ya yi wani abin da ya fi haka?


Duk abin da zai kasance a nan gaba ga Roy, zai so ya ƙare wannan kakar tare da nasara kuma mummunan rikodin Nottingham Forest ya sa ƙungiyarsa ta fi kamata data lashe wasan, musamman da Eberechi Eze a irin wannan kyakkyawan yanayin na Eagles.


Forest ta samu nasara daya kacal daga cikin wasannin gasar 18 da ta yi a waje zuwa yanzu - a Southampton a watan Janairu - kuma ta samu maki bakwai gaba daya.


Wannan wasa ne mai wahala amma Palace tana gida kuma wannan na iya zama wasan karshe na Hodgson a matsayin koci - kawo yanzu yanzu. Ina tsammanin za su ba wa wannan dattijon nasara. 


Palace vs Nott Forest  2-0 


Everton vs Bournemouth

A zahiri ina jin kamar wannan wasa ne mai ban tsoro ga Everton. Makomarsu tana hannunsu kuma ina ganin zasu tsaya tsayin daka, amma Bournemouth zata basu wahala.


Everton za ta taka leda da karfi amma suna da damuwa kan ko Dominic Calvert-Lewin zai samu damar buga wasan.


Sabanin haka, matsayin Bournemouth yana nufin za su iya yin wasa da ƙarin 'yanci kuma hakan yana sa su zama masu haɗari.


Goodison Park zai kasance wuri mai cike da tashin hankali a cikin 'yan mintoci kaɗan na ƙarshe idan wannan wasan ya yi kusa kamar yadda nake tsammanin zai kasance, saboda ina tsammanin sakamako a wasu wurare yana nufin Everton ta yi nasara don tsayawa a gasar.


Ka zalika Everton ta sami babbar nasara a Brighton makonni biyu da suka gabata wanda ya taimaka ya sanya su cikin wannan yanayin. Tabbas sun tada wasansu a karkashin Sean Dyche, koda kuwa ba sa wasa akai-akai. Suna gida, a gaban magoya bayansu don haka za su tashi don wannan kuma ina tsammanin za su sami abin da suke bukata. Ina ganin za su ci 2-0 da farko amma na baiwa Bournemouth kwallo, saboda ina ganin har yanzu za a yi yar drama da tashin hankali. 


Everton vs Bournemouth   2-1


Leeds vs Tottenham

Kocin Leeds Sam Allardyce ya yanke kauna saboda yadda kungiyarsa ke da rauni a bayansa kuma wasanni uku ne kawai ya jagoranci kungiyar.


Shi ya sa ba zan iya ganin Leeds zatayi iya nasara a wannan wasan ba - kuma ina ganin zasu iya tafiya relegation.


Ko da yake Tottenham ba ta cancanci yabo da yawa ba. Ba kasafai suke taka leda mai kyau ba a kakar wasa ta bana wanda bana ganin zasu samu nasarar da za ta ba su damar zuwa matsayi na bakwai domin zuwa Turai a kakar wasa mai zuwa.


Leeds vs Tottenham  2-2


Leicester vs West Ham

Wani abin mamaki game da Leicester da Leeds shine duka biyun sun zira kwallaye da yawa, fiye da kowa a kasan rabin teburin gasar. Leicester ta zura kwallaye 49, wanda ya kai yawan kwallayen Aston Villa, wacce ke matsayi na bakwai.


Amma su duka biyun sun kasance m basu da kyakykyawan tsaro a baya, shi ya sa suke kasa a can.


Leicester ta yi caca cewa za su iya yin kunnen doki suka raba maki da Newcastle, idan suka yi nasara a wannan wasa za su iya tsayawa a gasar. Ina tsammanin sassan wasan biyu na farko za su tafi bisa ga tsari, amma abin bakin ciki na karshe ya fita daga hannunsu kuma nasara a nan bazata isa ta cece su ba.


West Ham na iya jujjuya 'yan wasan ta da za su buga wasan karshe na gasar cin kofin Europa, amma duk da haka ba su da kyau. Sun tafi daga karshen watan Agusta zuwa farkon Afrilu ba tare da gudanar da nasarar gasar ko daya a kan hanya ba.


Leicester vs West Ham  2-1 


Man Utd vs Fulham

Fulham ta buga kyakykyawan wasa a wasan karshe da suka yi a Old Trafford a gasar cin kofin FA a watan Maris, kafin abubuwan su canja musu cikin sauri.


Ina ganin kungiyar Marco Silva za ta buga wasan a wannan karon ma. United ta tabbatar da samun gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa bayan da ta doke Chelsea da ci 4-1 a ranar Alhamis kuma na tabbata wasan karshe na cin kofin FA na karshen mako mai zuwa zai kasance a zuciyarsu.


Kungiyar Erik ten Hag sun dan ratsa kan layi a tseren na manyan hudun farkon gasar, amma tsarin wasanninsu na gida sun kasance mai ƙarfi Kuma mai kyua kuma yakamata su sake samun nasara akan Fulham a wannan karon ma.


Fulham za ta kare a mataki na 10 da duk irin sakamakon da aka samu - sun yi kakar wasa mai kayatarwa kuma ina jin dadin kallon su. 


Man Utd vs Fulham   2-0


Southampton vs Liverpool

Southampton ba ta da abubuwan tunawa masu dadi da zasu iya waiwaya baya a kakar wasa ta bana, musamman a gida inda sau biyu kawai ta yi nasara a duk kakar gaba daya.


Ta kasance kaka mai wahala ga kungiyar Jurgen Klopp suma kuma rashin buga gasar cin kofin zakarun Turai babban abin takaici ne a gare su, amma a kalla za su kare da dan kwarin gwiwwa.


Ina sa ran Mohamed Salah zai zura kwallo a raga, Liverpool kuma za ta yi nasara.


Kasa lika tuni Southampton ta yi kasa a gwiwa amma ba su yi karo da Brighton gaba daya ba a makon da ya gabata a wasansu na farko tun bayan da suka koma matakin relegation. Zai iya bambanta da Liverpool, ko da yake, saboda kungiyar Jurgen Klopp za ta ji yunwa don ci gaba da nuja kyakkyawan tashen da sukeyi kuma ina ganin zasu iya zira kwallaye kaɗan.


Southampton vs Liverpool        0-3


Comments