Min menu

Pages

Makomar: Rashford, Bellingham, Lukaku, Neves, Solomon, Boey, Saka, Origi

 

Musayar yan wasa a yau ranar Lahadi makomar: Rashford, Bellingham, Lukaku, Neves, Solomon, Boey, Saka, Origi


Ga kanun labaran

Kocin Manchester United Erik Ten Hang na da kwarin gwiwwar Dan wasan kungiyar Marcus Rashford zai sabunta kwantiraginsa a kungiyar, Madrid zata dau Bellingham akan kudi 100m pound, Liverpool ta shiga cinikin Neves Yana daf tafiya Barcelona, sabon kocin Chelsea zai tantance Lukaku, Origi nason dawowa Premier league


Ga cikakken labarin 

Kocin Manchester United Erik ten Hag yana tsammanin dan wasan gaban Ingila Marcus Rashford mai shekaru 25 zai tsawaita kwantiraginsa wanda zai kare a karshen kakar wasa mai zuwa. (Viaplay via Manchester Evening News)


Real Madrid za ta sayi dan wasan tsakiya na Ingila Jude Bellingham, mai shekaru 19, daga Borussia Dortmund kan yarjejeniyar da ta kai kusan fan miliyan 100. (Sunday Mirror)


Sabon kocin Chelsea Mauricio Pochettino na son tantance Romelu Lukaku. Dan wasan gaban Belgium mai shekaru 30, wanda zaman aronsa zai kare a Inter Milan a bazara, inda Dan wasan yake son ci gaba da zama a kulob din Italiya. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)


Chelsea na dab da sayen dan wasan bayan Lisbon dan kasar Uruguay Manuel Ugarte, mai shekaru 22, amma kuma Liverpool ma na zawarcin Dan wasan. (Franco Fernandez via Express)


Liverpool ta nemi a sanar da ita halin da Wolves dan wasan kasar Portugal Ruben Neves, mai shekaru 26 yake, Wanda zai shiga shekarar karshe ta kwantiraginsa kuma ana alakanta shi da Barcelona. (Football Insider)


Aston Villa, Newcastle United, Tottenham da Roma za su iya duba dan wasan gaban Wolves mai shekaru 27 Hwang Hee-chan saboda suna iya siyar da 'yan wasa don biyan ka'idojin daidaiton kudi (FFP). (Sunday Mirror)


Tottenham na duba yiwuwar zawarcin dan wasan Isra'ila Manor Solomon, wanda ke taka leda a Fulham, bayan da Fifa ta ce dan wasan mai shekaru 23 zai iya barin Shakhtar Donetsk a kyauta a wannan bazarar. (Athletic - subscription required)


Arsenal na tunanin zawarcin dan wasan bayan Galatasaray dan kasar Faransa Sacha Boey, mai shekaru 22. (Sunday Telegraph - subscription)


Arsenal ta ki saka batun sakin sabon kwantiragin dan wasan gaban Ingila Bukayo Saka mai shekaru 21, a maimakon haka ta ba shi gajeriyar kwantiragin fiye da yadda aka zata, wanda zai kare har zuwa 2027. (Mail on Sunday).


Burnley na sa ido kan dan wasan Liverpool dan kasar Portugal Fabio Carvalho, mai shekaru 20, kuma a shirye suke su dauke shi na dindindin ko kuma a matsayin aro. (Football Insider)


Dan wasan gaban Belgium Divock Origi, mai shekaru 28, na shirin barin AC Milan kuma, yayin da kungiyoyi a Turkiyya ke zawarcinsa, amma ya fi son komawa gasar Premier. (Il Corriere dello Sport via Football Italia)


Brighton na tattaunawa don siyan golan Livingston na Amurka Brian Schwake, mai shekaru 21, yayin da golan Spain Robert Sanchez mai shekaru 25, ke tunanin makomarsa a kungiyar. (Mail on Sunday)


Andoni Iraola, wanda Leeds United ke nema, zai bar aikinsa na kocin Rayo Vallecano. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Comments