Min menu

Pages

WASU ABUBUWA GUDA BIYAR DA SUKA SANYA MUTANE SUKE SON AMFANI DA KAFAR SADARWA TA WHATSAPP


 WASU ABUBUWA GUDA BIYAR DA SUKA SANYA MUTANE SUKE SON AMFANI DA KAFAR SADARWA TA WHATSAPP

Akwai wasu dalilai guda biyar dake sa mutane son yin amfani da whatsApp,tun bayan ɓacewar togo daga nan whatsApp shikuma ya Kunno Kai wanda ayanzu yana daga cikin manyan kamfanonin sadarwa wanda suka shahara a duniya kuma mutane suke yawan amfani dashi maza da mata,manya da yara zaka ga mutum koda wayarsa bata da whatsApp ɗin to zai rabu da ita, sakamakon yanzu kowa yana yin whatsApp aka waɗannan dalilin guda biyar wanda zanyi bayanin su kamar haka

  1. Business

Kasuwanci yanzu ya koma Online a ko'ina kake zaka turawa mutum sample na kayan da ake so ta cikin whatsApp shi kuma ya duba ya zabi wanda yake sai yayi maka reply,kai kuma ka tura masa da kayan a duk inda yake ba tare da kaje wurinsa ba ko kuma yazo wurinda kake.

  1. VIDEO CALL DA VOICE CALL

Video call ko kuma voice a yanzu sunfi ka kira mutum to kan layinsa saukin jan kuɗi kuma zaka iya kiransa a kowace ƙasa yake a duniya nan.misali zaka idan zaka saka kati na ₦100 ka kira mutum kuyi minti goma dashi to idan data ka saka ka kirashi ta whatsApp zaku iya minti 60 kuma datar baza kare ba.hakan dai idan kayi masa video call zaka ganshi kuma shima zai ganka wanda hakan baya yiwuwa a kiran da ake yi ta airtime.

  1. HIRA A SIRRANCE (PRIVACY)

Privacy wato zaka iya hira da mutum a whatsApp a sirrance ta yanda babu wanda zai me kuke tattaunawa a tsakaninku ko da kuwa kamfanin whatsApp ɗin bazai sani ba.zaka iya hanawa a ganka online a whatsApp ɗin zaka iya hanawa a saka ka acikin group ko kuma hana ana ganin last seen naka ko kuma iya boye chat dinka da wani ko wata ta yanda koda anshiga cikin whatsApp ɗin babu wanda zai gani.

       4 WHATSAPP GROUP 

whatsApp group yana da amfani sosai domin wata matattara ce wadda zata haɗa adadin wasu mutane wanda kuke so ku gani aciki,zaku iya haɗawa iya tsakanin family ko abokai ko iya ƴan makaranta ko iya ƴan kasuwa ka dai abinda yayi kama da hakan.

       5. SADA ZUMUNCI A TSAKANINKU

Idan kana da lambata ina da taka lambar to daga nan zamu iya sada zumunci a tsakaninmu ko da kana ina kuwa.koda ba bamayin magana ba to zanga status naka zaka ga nawa idan ka saka ko saka.

Comments