Min menu

Pages

 


Yanda zakayi control din wayar ka batare da ka taba ta ba.

Assalamu alaikum barkan mu da kasancewa a daidai wannan lokachi. Ina fatan mun kara samun kowa cikin kwanciyar hankali da walwala. Allah ya qaro mana jindadi ya yaye mana abinda ya dame mu ameen.

Yan'uwa yau darasin mu kan wani application ne da zai baka damar control ko ince da hausa amfani da wayar ka batare da ka taba ta ba. 

Nasan da yawa mutane su kanso suji cikakken bayani akan wannan application din. To kada ku damu ku biyo mu insha Allah zamuyi muku cikakken bayani.

Wannan application zai baka damar amfani da wayar ka batare da ka taba wani bangare na wayar ba.

Sau dadama zaka iya wayar gari kaga wayar ka wani abu bayayi misali wani bangare na screen din ka ko kuma wajen danna Volume duka biyun ko gaba daya ma wajen kashe wayar zakga baya aiki sosai.

Hakan yake sawa muyum ta dole sai ya chanja wayar kuma gashi wayar yana son ta ko kuma ma gaba daya bashi da kudin wata wayar. Sai de ya kai gyaran ta a haka ma watakila a gama bashi wuya kuma ya zamto a karshe wayar ta qi gyaruwa.

To idan kayi amfani da wannan application din zaka iya saita duk yanda kake so wayar ka tayi ma batare da kana amfani da duk wani sassa na wayar ba.

Zan ajje muku link din wannan application a kasa sai kuje ku sauke wannan application a wayar ku.

Kana  dakko wannan application din gaba daya bashi da wuya wajen amfani da shi. Domin kana budewa kawai zai baka damar saita duk wani sassa na wayar domin ya sauwa ke ma amfani da wayar taka.

Nasan wani zaice to taya za'ayi amfani da application bayan screen din baya dannuwa. Ida kayi kokari ka dakko application din to zai dan Makalema a gefen wayar taka domin fara amfani da shi.

Saboda haka kaje kasa zakaga na ajje wani link an rubuta Download sai ka taba ka sauke wannan application din a wayar ka.

👇👇👇👇👇👇

Download