Min menu

Pages

Yadda zakuyi hoto ko bidiyo koda wurin da kuke babu haske kuma yayi kyau sosai

 

 Yadda zakuyi hoto ko bidiyo koda wurin da kuke babu haske kuma yayi kyau sosai

 


 Assalamu Alaikum..

 

 Yn uwa barkanmu da wannan lokaci, barkanmu da sake kasancewa daku a wani sabon shirin.


A yau cikin shirin namu mun kawo muku wani application dazai baku damar yin hoto ko bidiyo koda kuna a cikin duhu, kuma kuga kamar da rana kuka dauka.


Wannan app din zai taimaka musamman ga wadanda wayoyinsu basu da kyakykyawar kamerar daukar hoto, zasu iya yin hoto ko bidiyo kuma ya gyara musu shi.


Application ne dazai fitar muku da hoto ko bidiyonku da kuka dauka a cikin duhu kuma ya gyara muku shi ya sanya ma hotunanku ko bidiyos dinku filters da sauran kayan gyaran hoto.


Sannan yana zuko haske da kansa ya fitar muku da hotonku ko bidiyonku a wurin da yake da karancin haske.


Yayin da zaku dauki dukkan hoto ko bidiyo ya kasance wayarku tana wuri daya ma’ana kada ku motsa ta ko kuma ku girgizata


Sunan wannan application din Night Vision Camera app, yana da saukin amfani da zarar kun dauko shi zaku iya fara amfani dashi kai-tsaye kamar yanda normal camera take. Zaku iya sauke app din anan kasa inda aka rubuta danna nan domin dauko shi.


Danna nan

Mun gode. 

Comments