Min menu

Pages

Yadda zaka mayar da fasalin wayarka irin na iPhone 14 Pro

 

 Yadda zaka mayar da fasalin wayarka irin na iPhone 14 Pro Assalamu Alaikum,

 En uwa barkanmu da wannan lokacin, ya kuke ya hakurin kasancewa damu.

A cikin shirin namu nayau munzo muku ne da wani application dazai birgeku sosai ta yanda zai mayar muku da tsarin wayarku irin na iPhone 14 pro.

Wannan application din zai saukake maka samun yanda fasalin iPhone 14 pro yake akan wayarka ta Android.

Shidai wannan application sunansa dynamic spot an tsara shine domin yayi iri daya dana iPhone 14 pro. Tare da wannan application din zaka iya shiga dukkan irin features din da iPhone 14 pro take dashi a wayarka ta Android kaima.

Zai kuma kara baka damar yin abubuwa a lokaci guda wato multitasking kuma zaka iya canza yanayin settings din wayarka zuwa wani fasalin daban.

Ba kamar yanda fasahar take akan iPhone 14 pro ba wato bazaka iya canza shi zuwa yanda kake so ba, amma application din dynamic spot zai baka damar canza komai kamar — shirya tsarin notification, music, calls da sauransu.

Zaku iya dauko wannan application din na dynamic spot akan Google play store ko kuma ku duba kasa inda aka rubuta download domin sauke shi.

Download

Kuci gaba da kasancewa damu.

Mun gode. 

Comments