Min menu

Pages

Yadda za kuyi kira kyauta
Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da wannan lokacin ya kuke ya hakurin kasancewa tare damu a yau cikin shirin namu munzo muku ne da bayanin wani application wanda zai baku damar yin kira kyauta a cikin wayoyinku.

Idan aka ce kyauta to ana nufin mutum ba zayyi amfani da kudi ba wajen gabatar da wannan kiran.

To saidai mutum sai yabi wasu hanyoyi tukunna koda ya mallaki wannan application din.


Da farko sunan application din Free call daga kun rubuta zaku ganshi cikin Play store saiku saukar dashi ko kuma ku duba kasa za kuga gurin da muka rubuta danna nan idan kuka danna zai kaiku gurin.

Idan kun bude shi zai kawo muku wannan fuskar kai tsaye saiku danna set phone number 


Idan kun zaba zai kawo muku fuskar da  take kasa

Mutum zaisa number wayarsa sannan zasu tura masa code sai yasa to amma za suce mutum sai ya credits kamar yadda a sama za kuga nawa inda aka sa my credit dinnan acan sama.

Hanyar da ake tara wannan credit din shine mutum zai danna wannan photon na farko inda kukaga 0 0 0 dinnan to zasu nuna muku dan karamin bidiyo na talla ko kuma mutum ya danna gunda aka rubuta watch rewarded ads dinnan.

Daga zarar ya tara credit din da suke bukata shikenan mutum zaiyi wayarsa cikin kwanciyar hankali.

Ga Link din saukar da wannan application din a kasa 

                    Danna nan

Comments

1 comment
Post a Comment

Post a Comment