Min menu

Pages

App din da zai ajiye muku dukkan bayanan da kuka rubuta a wayarku.

 App din da zai ajiye muku dukkan bayanan da kuka rubuta a wayarku.Assalamu alaikum da fatan kuna lafiya, sannunku da jimirin kasancewa tare damu.


Haƙiƙa muna jin dadin yadda kuke kasancewa tare damu kuma muna godiya sosai da sosai.


A ci gaba da kawo muku bayanai akan Application, yauma muna dauke muku ne da wani application wanda muka tabbatar zai birgeku idan kun mallakeshi.


         Menene sunan wannan App din?


Wannan App din sunansa typing key logger


                Menene amfaninsa?

Tun daga jin sunan wannan App din zaku fahimci na rubutu ne to saidai bawai rubutu kawai ake yi da app din ba kamar yadda wasu ke tsammani ba yana da wani amfani mai girma.


Amfaninsa shine duk lokacinda mutum yayi rubutu walau a Facebook ne ko a WhatsApp ko kuma yayi typing na wasu password ko wani abu shi wannan App din yana yin saving duk abinda mutum ya rubuta.Koda wata rana mutum zai samu matsala ya manta abinda ya rubuta to da zarar ya shiga cikin wannan App din to zai nuna masa dukkan abinda ya rubuta din da kuma ranar da yayi rubutun.


Koda an samu matsala mutum bashi da lafiya yadda bazai iya magana ba kuma ana son sanin wani abu daga gurinsa kuma ya taba rubutawa, kamar bayanan Bank wato password da sauransu, to daga zarar mutum ya shiga ciki insha Allah za'a gani.


Duk mai son dauko wannan App din ya duba kasa gurinda aka rubuta danna nan domin saukarwa 
                           Danna nan

Comments