Min menu

Pages

Website biyu masu matuqar amfani

 


Assalamu alaikum barkan mu da sake kasancewa da ku a yau a wani sabon darasin. Yau darasin namu yana da matuqar tsada domin zai baka damar mallakar wasu website wanda aka dade ana jiran irin su domin saukaka ma yanda zakayi edit na hoto batare da wata software ta computer ba.

 Duk da munyi bayanin cikaken darasin acikin videon kuma nasan da yawan ku kunzo ku mallaki wadannan website masu tsada. To zan ajje muku sunayen su a chan kasa domin kuma kuyi amfani da su.

Website na farko zai baka damar editing din hoton ka kamar a computer acikin wayar ka. Da yawa nasan munsan photoshop da kuma ayyukan sa da tsadar da yake dashi a computer to shi wannan website yana kama da computer sannan batare da ka mallaki wata computer ba. Ga sunan shi nan a kasa sai kaje kayi amfani da shi

👇👇👇👇👇

PHOTOPEA.Com


Website na biyu shima yana dauke da wani sirri ne na hada hoto musamman na DP idan zaka saka a wani social medai naka domin ya qawatar da abokan ka. Zaka zabi kalar wanda kake so kayi amfani da shi domin burgewa ga sauran mutane.

Kwata-kwata bashi da tsada ko wuya wajen amfani da shi saboda haka zan ajje muku sunan sa a kasa domin kuma kuyi amfani da wannan website din

👇👇👇👇👇👇

pfpmaker.com

Comments