Min menu

Pages

Ta whatsapp zaka ga inda budurwar ka take zuwa koda bata fadama ba

 


Assalamu alaikum ina muku barka da wannan lokachi. Yau darasin mu zamuyi bayani akan whatsapp da wasu sirrika ya zo da su wanda zai baka damar gane inda matar ka ko budurwar ka take zuwa.

Tuntuni na dora videon akan youtube da kuma facebook page dina. Saboda haka zan danyi qarin bayani ne anan. Duba da wasu sun fiso su karanta domin kallaon videon yana yi musu wuya.

Da farko de acikin videon nayi bayani ne akan wasu abubuwa guda uku na farko wanda zaka iya turawa mutum sako batare da kayi save din number sa ba. Kai koda ma baka shiga whatsapp ba zaka iya tura masa sakon.

Na biyu da na uku duk kusan abu daya ne sai de zan dan banbance muku su yanzu!. Akan location ne na whatsapp da zara kana so kayi amfani da location na bin diddigin mutum to abin ya kasu shi biyu ne shine zan dan yi muku bayanin su a takaice.

1) Idan kana son turawa mutum sako a whatsapp batare da kayi save din number sa ba abinda zakayi shine. Zaka nemo browser bayan ka nemo shine zakayi search din (wa.me/+234) wato WA.ME/ sune abinda ya kamata ku riqe domin +234 din code ne na kasa. kuma kowace kasa tana da code dinta. Wannan +234 code din nigeria ne. bayan ka saka WA.ME/+234sai ka saka number mutum a jikin code din kasar da number take misali : WA.ME/+2347033456749 to da zarar ka dannan shine direct zaka turawa da wannan number sako batare da kayi save din number ba.

2) Wannan zan hade muku bayanin su gaba daya domin ku fahimta. Na farko idan kana so kayi amfani da locatiom a whatsapp bayan ka shga inda kuke chat da mutum to zaka nemo location bayan ka taba kuma ya bude ma zakaga Share live location sannan zakaga Current location. Amman idan location din wayar ka ba abude yake ba to dole zai munama saia ka bude to sai ka kunna shi.

Shi wanna Share Live location din shine idan ka turawa wani family naka ko kuma a wayar matar ka ko budurwar ka ka amsa ka turo ta lambar ka amfanin sa shine. Za'a iya bin diddigin ka duk inda kake zuwa. har tsayon lokachin da aka saita wannan location din. Misali koda ace akan titi kake tafiya kuma a kasa inde an shiga cikin wannan location din naka za'aga inda kake tafiya kuma koda tsayawa kayi siyan rake za'a ga ka tsaya. Koda wani gida ka shiga za'a ga ka shiga gidan ta wannan hanyar. Ina fatan kun fahimta.

Shi kuma Current location idan aka tura shi kawai zai fadi inda kake a lokachin da ka tura amman idan ka bar wajen koda an chi gba da duba wannan location din kawai iya inda ka nuna nan za'a gani. Shi baza'a bi diddigin ka ba. Kamar Live location. Wannan nasan ya gamsar da mai karantawa. 

Amman akwai cikakken videon akan facebook page da kuma youtube.

Nagode

Comments