Min menu

Pages

Karatu kyauta a Qatar: 2022

   Assalamu Alaikum Warahmatullah

 En uwa barkanmu da sake kasancewa daku a wani sabon shirin.

Ayau shirin namu yazo muku ne da wata scholarship a wata jami’ar kasar Qatar ta daliban da basajin yaren larabci.

Application na cike wannan scholarship suna gayyatar dukkan daliban duniya wadanda yarensu na asali ba larabci bane domin yin karatu a jami’ar Qatar.

Wata cibiya ce ta musamman ta koyar da harsuna wanda suke bada certificate ga daliban kasashen waje wadanda yaren iyayen su ba larabci bane.

Cibiyar tana da matakan koyar da yaruka har 6 a kowace shekara, tun daga kan kananan masu koyo na 1 zuwa manya na 2. Samun admission a tsarin ANNS a matsayin scholarship yana da wahala, amma duk wani applicants mai sha’awar cikewa sai dai ya nema a matsayin paying student

Daga nan ne jami’ar Qatar zata baiwa duk wani paying student visa ta dalibai idan applicant din ya cika sharudan student visa din kari da kiyaye sharudan admission.

Requirements

Domin samun admission a ANNS scholarship, dole:

• Dalibi ya kasance dan kasa da kasa wanda yarensa ba larabci bane.

• Dalibi ya mallaki mafi karanci high school diploma.

• Dalibi ya kasance tsakanin shekaru 18 zuwa 40.

• Sannan dalibi ya kasance zai iya magana da kodai yaren turanci ko larabcin tare da shuwagabanni da al’ummar makarantar.

Reward

• Wannan scholarship ta hadar da biyan kudin karatu da littattafai.

• Biyan kudin student visa.

• Round-trip da kudin jirgi.

• Wurin kwana a cikin jami’ar daya hada da cin abinci sau uku a kowace rana (breakfast, lunch da dinner), injin wanki, free internet service, wurin wasanni, library, computer lab, wurin motsa jiki da sauransu.

Required Documents

Yayin cike wannan scholarship dole candidates su shirya bada wadannan takardun;

• Form din application (acike shi online)

• Kwafin attestation na takardun makarantar dakayi (tare da fassarar su da turanci ko larabci idan  bada turancin ko larabci suke ba. )

• CV/ Resume

• Kwafin passport

• Wasikar recommendation

• Hoton personal (kwafi 1), passport size

Dukkan applicants wadanda suke da ilimi ko yaya ne akan larabci zasu karbi girmamawa sama da wadanda basu da shi (ilimi akan bakaken larabci da kuma rubutu da karatu).

Domin samun karin bayani da yanda za’a cike wannan scholarship din a danna link din dake kasa.

Danna nan

Fatan Nasara.


Comments