Min menu

Pages

Da wannan App din zaka iya canja maganarka zuwa rubutu ko duk yaren da kake so

 

 Da wannan App din zaka iya canja maganarka zuwa rubutu ko duk yaren da kake soAssalamu alaikum yan uwa barkanmu da wannan lokacin ya kuke ya hakurin kasancewa tare damu?


Muna matukar jin dadin yadda kuke kasancewa tare damu kuma muna godiya sosai da sosai.


A yau cikin shirin namu munzo muku ne da bayanin wani application mai matukar kyau wanda zai baku damar juya maganarku zuwa duk yaren da kuke so.


Wannan App din zai taimaka ga duk wasu wanda suke son juya maganarsu zuwa wani yaren.


Baya da haka wannan App din zai zai taimaka muku wajen yin magana, kamar ka san magana ko zaka iya furta magana amma kuma baza ka iya rubutawa ba, to wannan application din zai rubuta muku daga zarar kun fadi kalmar da bakinku.


Haka zalika idan ka iya rubutawa kuma baka iya furatawa ba duka wannan App din zai furta maka daga zarar ka rubuta.


Sannan cikin App din akwai dictionary wanda zai taimaka wajen saukaka muku a neman kalmar.


Ku duba kasa gurinda aka rubuta danna nan domin sauke wannan App din 


                          Danna nan


                         Danna nan 

Comments